49
Bawan Ubangiji
Ku kasa kunne gare ni, ku tsibirai;
ku ji wannan, ku al’ummai masu nesa.
Kafin a haife Ni Ubangiji ya kira ni;
tun daga haihuwata ya ambaci sunana.
Ya yi bakina kamar takobi mai kaifi,
cikin inuwar hannunsa ya ɓoye ni;
ya sa na zama kamar kibiya mai tsini
ya kuma ɓoye ni cikin kwarinsa.
Ya ce mini, “Kai bawana ne,
Isra’ila, a cikinka zan bayyana darajata.”
Amma na ce, “Na yi aiki a banza;
na kashe duk ƙarfina a banza da wofi.
Duk da haka abin da yake nawa yana a hannun Ubangiji,
ladana kuma tana a wurin Allahna.”
Yanzu fa Ubangiji ya ce
ya siffanta ni a cikin mahaifa don in zama bawansa
don in dawo da Yaƙub gare shi
in kuma tattara Isra’ila gare shi,
gama an girmama ni a gaban Ubangiji
Allahna kuma ne ƙarfina
ya ce,
“Ɗan ƙaramin abu ne ka zama bawana
don ka maido da kabilar Yaƙub
ka kuma dawo da waɗannan na Isra’ilawan da na kiyaye.
Zan kuma mai da kai haske ga Al’ummai,
don ka kawo cetona zuwa iyakokin duniya.”
 
Ga abin da Ubangiji yana cewa,
Mai Fansa da kuma Mai Tsarkin nan na Isra’ila
gare shi wanda al’ummai suka rena suka kuma ki,
ga bawan masu mulki.
“Sarakuna za su gan ka su kuma miƙe tsaye,
sarakuna za su gani su kuma rusuna,
saboda Ubangiji, wanda yake mai aminci,
Mai Tsarkin nan na Isra’ila, wanda ya zaɓe ka.”
Maidowar Isra’ila
Ga abin da Ubangiji yana cewa,
“A lokacin tagomashina zan amsa muku,
kuma a ranar ceto zan taimake ku;
zan kiyaye ku zan kuma sa
ku zama alkawari ga mutane,
don ku maido da ƙasa
ku kuma sāke raba gādon kufai,
don ku ce wa waɗanda suke cikin kurkuku, ‘Ku fito,’
ga waɗanda suke cikin duhu kuma, ‘Ku ’yantu!’
 
“Za su yi kiwo kusa da hanyoyi
su kuma sami wurin kiwo a kowane tudu.
10 Ba za su taɓa jin yunwa ko ƙishi ba,
ba kuwa zafin hamada ko rana ta buge su ba.
Shi da ya yi musu jinƙai zai jagorance su
ya kuma bishe su kusa da maɓulɓulan ruwa.
11 Zan mayar da dukan duwatsu su zama hanyoyi,
a kuma gyara manyan hanyoyina.
12 Duba, za su zo daga nesa
waɗansu daga arewa, waɗansu daga yamma,
waɗansu daga yankin Aswan.”*
 
13 Ku yi sowa don farin ciki, ya ku sammai;
ki yi farin ciki, ya ke duniya;
ku ɓarke da waƙa, ya ku duwatsu!
Gama Ubangiji ya ta’azantar da mutanensa
zai kuma ji tausayin mutanensa da suke shan wahala.
 
14 Amma Sihiyona ta ce, “Ubangiji ya yashe ni,
Ubangiji ya manta da ni.”
 
15 “Yana yiwuwa mahaifiya ta manta da jariri a ƙirjinta
ta kuma kāsa nuna tausayi ga yaron da ta haifa?
Mai yiwuwa ta manta,
amma ba zan taɓa manta da ke ba!
16 Duba, na zāna ki a tafin hannuwana;
katangarki kullum suna a gabana.
17 ’Ya’yanki maza su komo da gaggawa,
waɗanda suka lalatar da ke kuwa za su bar ki.
18 Ki ɗaga idanunki ki duba kewaye;
dukan ’ya’yanki sun taru suka kuma dawo gare ki.
Muddin ina raye,” in ji Ubangiji,
“Za ki yafa su duka kamar kayan ado;
za ki yi ado da su, kamar amarya.
 
 
19 “Ko da yake an lalatar da ke aka kuma mai da ke kufai
ƙasarki kuma ta zama kango,
yanzu za ki kāsa sosai saboda yawan mutanenki,
kuma waɗanda suka cinye ki za su kasance can da nisa.
20 ’Ya’yan da aka haifa a lokacin baƙin cikinki
za su ce a kunnenki,
‘Wannan wuri ya yi mana kaɗan ƙwarai;
ki ƙara mana wurin zama.’
21 Sa’an nan za ki ce a zuciyarki,
‘Wa ya haifa waɗannan?
Na yi baƙin ciki na kuma zama wadda ba ta haihuwa;
an yi mini daurin talala aka kuma ƙi ni.
Wane ne ya yi renon waɗannan?
An bar ni ni kaɗai,
amma waɗannan, ina suka fito?’ ”
22 Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce,
“Duba, zan yi alama wa Al’ummai,
zan ɗaga tutana wa mutane;
za su kawo ’ya’yanki maza a hannuwansu
su riƙe ’ya’yanki mata a kafaɗunsu.
23 Sarakuna za su zama kamar iyayen reno,
sarauniyoyinsu kuma za su yi renonku kamar uwaye.
Za su rusuna a gabanki da fuskokinsu har ƙasa;
za su lashe ƙura a ƙafafunki.
Sa’an nan za ki san cewa ni ne Ubangiji;
waɗanda suke sa zuciya gare ni ba za su sha kunya ba.”
24 Za a iya ƙwace ganima daga jarumawa,
ko a kuɓutar da kamammu daga hannun marasa tsoro?
25 Amma ga abin da Ubangiji yana cewa,
“I, za a ƙwace kamammu daga jarumawa,
a kuma karɓe ganima daga hannun marasa tsoro;
zan gwabza da waɗanda suke gwabzawa da ke,
zan kuwa ceci ’ya’yanki.
26 Zan sa masu zaluntarki su ci naman jikinsu;
za su bugu da jininsu, sai ka ce sun sha ruwan inabi.
Sa’an nan dukan mutane za su sani
cewa ni, Ubangiji, ni ne Mai Cetonki,
Mai Fansarki, Maɗaukakin nan na Yaƙub.”
* 49:12 Littattafan Bahar Rum; Rubuce-rubucen Masoretik suna da Sinim