35
Farin cikin waɗanda aka ceta
Hamada da ƙeƙasasshiyar ƙasa za su yi murna;
jeji zai yi farin ciki ya kuma hudo.
Kamar fure, zai buɗu ya hudo;
zai yi farin ciki mai girma ya kuma yi sowa don farin ciki.
Za a maido wa Lebanon da darajarta,
darajar Karmel da Sharon;
za su ga ɗaukakar Ubangiji,
darajar Allahnmu.
Ku ƙarfafa hannuwa marasa ƙarfi,
ku ƙarfafa gwiwoyin da suka gaji;
ku faɗa wa waɗanda suka karai a zukata,
“Ku yi ƙarfin hali, kada ku ji tsoro;
Allahnku zai zo,
zai zo domin ya ɗau fansa;
da ramuwar Allah
zai zo don yă cece ku.”
 
Sa’an nan idanun makafi za su buɗe
kunnuwan kurame kuma su ji.
Sa’an nan guragu za su yi tsalle kamar barewa,
bebaye kuma su yi sowa don farin ciki.
Ruwa zai kwararo daga jeji
rafuffuka kuma a cikin hamada.
Yashi mai ƙuna zai zama tafki,
ƙeƙasasshiyar ƙasa kuma za tă cika da maɓulɓulan rafuffuka.
A mazaunin diloli, inda suka taɓa zama,
ciyawa da iwa da kyauro za su yi girma.
 
Kuma babbar hanya za tă kasance a can;
za a ce ta ita Hanyar Mai Tsarki.
Marasa tsarki ba za su yi tafiya a kanta ba;
za tă zama domin waɗanda suka yi tafiya a wannan Hanya ce;
mugaye da wawaye ba za su yi ta yawo a kanta ba.
Zaki ba zai kasance a can ba,
balle wani naman jeji mai faɗa ya haura kanta;
ba za a same su a can ba.
Amma fansassu ne kaɗai za su yi tafiya a can,
10 kuma fansassu na Ubangiji za su komo.
Za su shiga Sihiyona da rerawa;
matuƙar farin ciki zai mamaye su.
Murna da farin ciki za su sha kansu,
baƙin ciki kuma da nishi za su gudu.