33
Damuwa da taimako
Kaitonka, ya kai mai hallakarwa,
kai da ba a hallakar da kai ba!
Kaitonka, ya maciya amana,
kai da ba a ci amanarka ba!
Sa’ad da ka daina hallakarwa,
za a hallaka ka;
sa’ad da ka daina cin amana,
za a ci amanarka.
Ya Ubangiji, ka yi mana jinƙai;
muna marmarinka.
Ka zama ƙarfinmu kowace safiya,
cetonmu a lokacin damuwa.
Da tsawar muryarka, mutane za su gudu;
sa’ad da ka tashi, al’ummai za su watse.
Ganimarku, ya al’ummai ƙanana fāri sun girbe;
kamar tarin fārin da mutane sun fāɗa wa.
 
Ubangiji da girma yake, gama yana zaune a bisa;
zai cika Sihiyona cikin gaskiya da adalci.
Zai zama tabbataccen harsashi na koyaushe,
ma’ajin ceto da hikima da sani a yalwace;
tsoron Ubangiji shi ne mabuɗin wannan dukiya.*
 
Duba, jarumawansu suna kuka da ƙarfi a tituna;
jakadun salama suna kuka mai zafi.
An gudu an bar manyan hanyoyi,
babu matafiye a kan hanyoyi.
Aka keta yarjejjeniya,
an rena shaidunsa
ba a kuwa ganin girman kowa.
Ƙasa tana kuka an kuma gudu an bar ta,
Lebanon ta sha kunya ta kuma yanƙwane;
Sharon ta zama kamar Araba,
Bashan da Karmel sun kakkaɓe ganyayensu.
 
10 “Yanzu zan tashi,” in ji Ubangiji.
“Yanzu ne za a ɗaukaka ni;
yanzu za a ɗaga ni sama.
11 Kun yi cikin yayi,
kuka haifi kara;
numfashinku wuta ne da zai cinye ku.
12 Za a ƙone mutane kamar da ƙuna farar ƙasa;
kamar ƙayayyuwan da aka sare aka kuma sa musu wuta.”
 
13 Ku da kuke da nesa, ku ji abin da na yi;
ku da kuke kusa, ku san ikona!
14 Masu zunubi a Sihiyona sun firgita;
rawar jiki ya kama marasa sanin Allah suna cewa,
“Wane ne a cikinmu zai iya zama da wuta mai ci?
Wane ne a cikinmu zai iya zama da madawwamiyar ƙonewa?”
15 Shi da yake tafiya cikin adalci
yana kuma magana abin da yake daidai,
wanda yake ƙin riba daga cuta
yana kuma kiyaye hannunsa daga karɓan cin hanci,
wanda yake hana kunnuwansa daga ƙulla kisa
ya kuma rufe idanunsa a kan tunanin aikata mugunta,
16 shi ne mutumin da zai zauna a bisa,
wanda mafakarsa za tă zama kagarar dutse.
Za a tanada abincinsa, kuma ruwa ba zai kāsa masa ba.
 
17 Idanunku za su ga sarki a cikin kyansa
ku kuma hangi ƙasar da take shimfiɗe can da nisa.
18 Cikin tunaninku za ku yi tunani firgitar da ta faru tun dā kuna cewa,
“Ina hafsan nan?
Ina wannan wanda yake karɓar haraji?
Ina hafsan da yake lura da hasumiyoyi?”
19 Ba za ku ƙara ganin waɗannan mutane masu girman kai kuma ba,
waɗannan mutane masu magana da harshen da ba ku fahimta ba.
 
20 Ku duba Sihiyona, birnin shagulgulanmu;
idanunku za su ga Urushalima,
mazauni mai lafiya, tentin da ba za a taɓa gusar ba;
wanda ba a taɓa tumɓuke turakunsa ba,
ko a tsinke igiyoyinta.
21 A can Ubangiji zai zama Mai Iko Duka namu.
Zai zama kamar inda manyan koguna da rafuffuka suke.
Matuƙan jirgin ruwa ba za su kai wurinsu ba,
manyan jiragen ruwa ba za su yi zirga-zirga a kansu ba.
22 Gama Ubangiji ne alƙalinmu,
Ubangiji ne mai ba mu dokoki,
Ubangiji ne sarkinmu;
shi ne wanda zai cece mu.
 
23 Maɗaurinku sun kunce
ƙarfafan itacen jirgin ba su da kāriya,
fikafikan jirgin ba su buɗu ba.
Ta haka za a raba yalwar ganima
har ma guragu za su kwashe ganimar.
24 Ba wani mazauna a Sihiyona da zai ce, “Ina ciwo”;
za a kuma gafarta zunuban waɗanda suke zama a can.
* 33:6 Ko kuwa dukiya ce daga wurinsa