31
Kaiton waɗanda suke dogara ga Masar 
 
1 Kaiton waɗanda suka gangara zuwa Masar don neman taimako,  
waɗanda suke dogara ga dawakai,  
waɗanda suke dogara ga yawan kekunan yaƙinsu  
da kuma a girman ƙarfin mahayan dawakansu,  
amma ba sa dogara ga Mai Tsarkin nan na Isra’ila,  
ko ya nemi taimako daga Ubangiji.   
2 Shi ma yana da hikima kuma zai iya kawo masifa;  
ba ya janye kalmominsa.  
Zai yi gāba da gidan mugu,  
gāba da waɗanda suke taimakon masu aikata mugunta.   
3 Amma Masarawa mutane ne ba Allah ba;  
dawakansu nama da jini ne ba ruhu ba.  
Sa’ad da Ubangiji ya miƙa hannunsa,  
shi da yake taimako zai yi tuntuɓe  
shi da aka taimaka zai fāɗi;  
dukansu biyu za su hallaka tare.   
4 Ga abin da Ubangiji ya faɗa mini,  
“Kamar yadda zaki kan yi ruri  
babban zaki a kan abin da ya yi farauta,  
kuma ko da yake dukan ƙungiyar makiyaya  
sun taru wuri ɗaya a kansa,  
ba zai jijjigu ta wurin ihunsu ba  
ko ya damu da kiraye-kirayensu,  
ta haka Ubangiji Maɗaukaki zai sauko  
don yă yi yaƙi a kan Dutsen Sihiyona da kuma a kan ƙwanƙolinsa.   
5 Kamar tsuntsaye masu shawagi a sama  
haka Ubangiji Maɗaukaki zai kiyaye Urushalima;  
zai kāre ta ya kuma fanshe ta,  
zai ‘ƙetare’ ta ya kuma kuɓutar da ita.”   
6 Ku dawo gare shi ku da kuka yi masa babban tayarwa, ya Isra’ilawa.  
7 Gama a wannan rana kowannenku zai ƙi gumakan azurfa da zinariya da hannuwanku masu zunubi suka yi.   
8 “Za a karkashe Assuriyawa da takobin da ba na yin mutum ba;  
takobi, da ba na yin mutum ba, zai cinye.  
Za su gudu daga takobi  
za a kuma sa samarinsu aikin dole.   
9 Kagararsu za tă fāɗi saboda razana;  
da ganin matsayin yaƙin, shugabannin yaƙinsu za su firgita,”  
in ji Ubangiji,  
wanda wutarsa tana a Sihiyona,  
wanda matoyarsa tana a Urushalima.