29
Kaiton birnin Dawuda
Kaitonki, Ariyel,* Ariyel
birnin da Dawuda ya zauna!
Ƙara shekara ga shekara
a kuma bar shagulgulanki su yi ta kewayewa.
Duk da haka zan yi wa Ariyel kwanto
za tă kuma yi kuka da makoki,
za tă zama mini kamar bagaden jini.
Zan kafa sansani kewaye da ke duka;
zan kewaye ki da hasumiyoyi
in tasar miki da ayyukan kwantona na yaƙi.
Za a ƙasƙantar da ke, za ki ƙi yin magana daga ƙasa;
maganarki za tă yi ƙasa-ƙasa daga ƙura.
Muryarki za tă zama kamar fatalwa daga ƙasa;
daga ƙura maganarki zai fito ƙasa-ƙasa.
 
Amma abokan gābanki masu yawa za su zama kamar ƙura mai laushi,
sojojinsu masu firgitarwa za su yi ta tashi kamar yayin da iska ta hura.
Farat ɗaya, cikin ɗan lokaci,
Ubangiji Maɗaukaki zai zo
da tsawa da rawar ƙasa da ƙara mai girma,
da hadarin iska da guguwa da harshe na wuta mai ci.
Sa’an nan sojojin dukan al’umman da suka yi yaƙi da Ariyel,
da suka fāɗa mata da kagararta suka kuma yi mata kwanto,
za su zama kamar yadda yake da mafarki,
wahayi da dare,
kamar sa’ad da mai yunwa yana mafarki cewa yana cin abinci,
amma sai ya farka, yunwan tana nan;
kamar sa’ad da mai ƙishirwa yana mafarki cewa yana shan ruwa,
amma sai ya farka yana suma, da ƙishinsa.
Haka zai zama da sojoji na dukan al’ummai
da suka yi yaƙi da Dutsen Sihiyona.
 
Ku firgita ku kuma yi mamaki,
ku makance kanku ku kuma zama a makance;
ku bugu, amma ba da ruwan inabi ba,
ku yi tangaɗi, amma ba daga barasa ba.
10  Ubangiji ya kawo muku barci mai nauyi,
Ya rufe idanunku (annabawa);
ya rufe kawunanku (masu duba).
11 Gare ku duk wannan wahayi ba kome ba ne sai dai maganganun da aka rufe a cikin littafi. In kuma kun ba da littafin ga wani wanda zai iya karanta, kuka kuma ce masa, “Karanta wannan, muna roƙonka,” zai amsa ya ce, “Ba zan iya ba; an rufe shi.” 12 Ko kuwa in kun ba da littafin ga wani wanda ba zai iya karantawa ba, kuka kuma ce, “Karanta wannan, muna roƙonka,” zai amsa ya ce, “Ban iya karatu ba.”
13 Ubangiji ya ce,
“Waɗannan mutane sun zo kusa da ni da bakinsu
suka kuma girmama ni da leɓunansu,
amma zukatansu suna nesa daga gare ni.
Sujadar da suke mini
cike take da dokokin da mutane suka koyar.
14 Saboda haka zan firgita waɗannan mutane sau ɗaya
da abubuwan banmamaki a kan abubuwan banmamaki;
hikimar masu hikima za tă lalace,
azancin masu azanci zai ɓace.”
15 Kaiton waɗanda suke zuwa manyan zurfafa
don su ɓoye shirye-shiryensu daga Ubangiji,
waɗanda suke aikinsu cikin duhu su yi tunani,
“Wa yake ganinmu? Wa zai sani?”
16 Kuna birkitar abubuwa,
sai ka ce an mayar da mai ginin tukwane ya zama yumɓu!
Abin da aka yi zai ce wa wanda ya yi shi,
“Ba shi ne ya yi ni ba”?
Tukunya za tă iya ce wa mai ginin tukwane,
“Ba ka san kome ba”?
 
17 Cikin ɗan lokaci, za a mai da Lebanon gona mai taƙi
kuma gona mai taƙi za tă zama kamar kurmi?
18 A wannan rana kurame za su ji maganganun littafi,
daga duruduru da duhu kuma
idanun makafi za su gani.
19 Masu tawali’u za su sāke yin farin ciki a cikin Ubangiji;
mabukata za su yi farin ciki cikin Mai Tsarkin nan na Isra’ila.
20 Masu zalunci za su ƙare,
masu ba’a za su ɓace,
kuma dukan waɗanda suke da ido don mugunta za su hallaka,
21 waɗanda ta magana kawai sukan mai da mutum mai laifi,
waɗanda suke kafa tarko wa mai ba da kāriya a ɗakin shari’a
da shaidar ƙarya kuma su hana marar laifi samun shari’ar adalci.
22 Saboda haka ga abin da Ubangiji wanda ya fanshi Ibrahim, ya ce wa gidan Yaƙub,
“Ba za a ƙara kunyata Yaƙub ba;
fuskokinsu kuma ba za su ƙara yanƙwanewa ba.
23 Sa’ad da suka ga ’ya’yansu a tsakiyarsu,
aikin hannuwansu,
za su kiyaye sunana da tsarki;
za su san tsarkin Mai Tsarkin nan na Yaƙub,
za su kuma ji tsoron Allah na Isra’ila.
24 Su da suke marasa azanci a ruhu za su sami fahimtar;
waɗanda suke gunaguni za su yarda da koyarwa.”
* 29:1 Ariyel. Wata ma’ana mai yiwuwa ta “ariyel” a Ibraniyanci za tă iya zama “Jarumi na Allah” ko kuwa “Zaki na Allah” ko kuma “Bagade na Allah.” 29:2 Ibraniyanci na bagaden jini ya yi kamar Ibraniyanci na Ariyel. 29:13 Da Ibraniyanci; Seftuwajin Suna mini sujada a banza; koyarwarsu ba kome ba ne illa dokokin da mutane suka koyar