22
Annabci a kan Urushalima
1 Abin da Allah ya faɗa game da Kwarin Wahayi.
Mene ne ya dame ku a yanzu,
da dukanku kuka hau kan rufin gidaje.
2 Ya kai gari cike da hayaniya,
Ya ke birnin tashin hankali da alkarya mai murna?
Mutanenki ba su mutu ta wurin takobi ba,
ba kuwa za su mutu a yaƙi ba.
3 Dukan shugabanninki sun gudu gaba ɗaya;
an kama su ba tare da an yi amfani da baka ba.
Dukanku da aka kama an kwashe ku ɗaurarru gaba ɗaya,
kun gudu tun abokin gāba yana da nisa.
4 Saboda haka na ce, “Ƙyale ni kurum;
bari in yi kuka mai zafi.
Kada ka yi ƙoƙarin ta’azantar da ni
a kan hallakar mutanena.”
5 Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki, yana da ranar
giggicewa da tattakewa da banrazana
a cikin Kwarin Wahayi,
ranar ragargazawar katanga
da ta yin kuka ga duwatsu.
6 Elam ya ɗauki kwari da baka,
tare da mahayan kekunan yaƙinta da dawakai;
Kir ta buɗe garkuwoyi.
7 Kwarurukanku mafi kyau sun cika da kekunan yaƙi,
an kuma tsai da mahayan dawakai a ƙofofin birni.
8 An rurrushe kāriyar Yahuda,
a ranan nan kuwa kun yi la’akari
da makamai a cikin Fadan Kurmi;
9 kuka ga cewa Birnin Dawuda
tana da wuraren kāriya masu yawa da suka tsattsage;
kuka tattara ruwa
a Tafkin Ƙasa.
10 Kuka ƙirga gine-gine a Urushalima
kuka kuma rurrushe gidaje don ku ƙarfafa katanga.
11 Kuka gina matarar ruwa tsakanin katanga biyu
saboda ruwan Tsohon Tafki,
amma ba ku yi la’akari da Wannan da ya yi su ba,
ko ku kula da Wannan da ya shirya shi tuntuni.
12 Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki
ya kira ku a wannan rana
don ku yi kuka ku yi ihu,
don ku aske gashinku ku kuma sa tsummoki.
13 Amma duba, sai ga shi kuna farin ciki kuna kuma murna,
kuna yankan shanu kuna kashe tumaki,
kuna cin nama kuna kuma shan ruwan inabi!
Kuna cewa, “Bari mu ci mu kuma sha,
gama gobe za mu mutu!”
14 Ubangiji Maɗaukaki ya bayyana wannan a kunnena cewa, “Har ranar mutuwarka ba za a yi kafarar wannan zunubi ba,” in ji mai girma Ubangiji Maɗaukaki.
15 Ga abin da Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki, ya faɗa,
“Je, ka faɗa wa wannan mai hidima,
Shebna, sarkin fada.
16 Mene ne kake yi a nan kuma wa ya ba ka izini
ka haƙa kabari wa kanka a nan,
kana fafe kabarinka a bisa
kana sassaƙa wurin hutunka a dutse?
17 “Ka yi hankali, Ubangiji yana shirin ya kama ka da ƙarfi
ya kuma ɗauke ka, ya kai mai ƙarfi.
18 Zai dunƙule ka kamar ƙwallo
ya jefa ka a cikin ƙasa mai girma.
A can za ka mutu
a can kuma kekunan yaƙinka masu daraja za su kasance,
abin kunya kake ga gidan maigidanka!
19 Zan tumɓuke ka daga makaminka,
za a kuma kore ka daga matsayinka.
20 “A wannan rana zan kira bawana, Eliyakim ɗan Hilkiya.
21 Zan rufe shi da rigarka in kuma yi masa ɗamara in miƙa masa ikonka. Zai zama mahaifi ga waɗanda suke zama a Urushalima da kuma gidan Yahuda.
22 Zan sa mabuɗin gidan Dawuda a kafaɗarsa; abin da ya buɗe ba mai rufewa, kuma abin da ya rufe ba mai buɗewa.
23 Zan kafa shi kamar turke a tsayayyen wuri; zai zama mazaunin daraja domin gidan mahaifinsa.
24 Dukan ɗaukakar iyalinsa za tă rataya a kansa daga ’ya’yansa da zuriyarsa har zuwa dukan ƙananan kayan aikinsa, wato, daga kwanoni har zuwa tuluna.
25 “A ranan nan, in ji Ubangiji Maɗaukaki, turken da aka kafa a tsayayyen wuri zai sumɓule; za a sare shi ya fāɗi, za a kuma datse nauyin da yake rataya a kansa.” Ni Ubangiji na faɗa.