2
Dutsen Ubangiji 
 
1 Ga abin da Ishaya ɗan Amoz ya gani game da Yahuda da Urushalima.   
   
 
2 A kwanaki masu zuwa  
za a kafa dutsen haikalin Ubangiji  
a matsayin babba cikin duwatsu;  
za a daga shi bisa tuddai,  
kuma dukan al’ummai za su bumbunto zuwa gare shi.   
3 Mutane da yawa za su zo su ce,  
“Ku zo, bari mu haura zuwa dutsen Ubangiji,  
zuwa gidan Allah na Yaƙub.  
Zai koya mana hanyoyinsa,  
domin mu yi tafiya cikin hanyoyinsa.”  
Dokar za tă fito daga Sihiyona,  
maganar Ubangiji daga Urushalima.   
4 Zai shari’anta tsakanin al’ummai  
zai kuma sulhunta faɗar mutane masu yawa.  
Za su mai da takubansu su zama garemani  
māsunsu su zama wuƙaƙen askin itatuwa.  
Al’umma ba za tă ƙara ɗauki takobi a kan al’umma ba,  
ba kuwa za su ƙara yin horarwar yaƙi.   
   
 
5 Ki zo, ya gidan Yaƙub,  
bari mu yi tafiya a hasken Ubangiji.   
Ranar Ubangiji 
 
6 Ka rabu da mutanenka,  
gidan Yaƙub.  
Sun cika da ayyukan sihiri da aka kawo daga Gabas;  
suna yin duba kamar Filistiyawa  
suna tafa hannuwa tare da marasa sanin Allah.   
7 Ƙasarsu ta cika da azurfa da zinariya;  
dukiyarsu kuma ba iyaka.  
Ƙasarsu ta cika da dawakai;  
kekunan yaƙinsu kuma ba iyaka.   
8 Ƙasarsu ta cika da gumaka;  
sukan rusuna ga aikin hannuwansu,  
ga abin da yatsotsinsu suka yi.   
9 Saboda an jawo mutum ƙasa  
aka kuma ƙasƙantar da ɗan adam,  
kada ku gafarta musu.   
   
 
10 Ku tafi cikin duwatsu,  
ku ɓuya cikin ƙasa  
daga razanar Ubangiji  
da kuma darajar ɗaukakarsa!   
11 Za a ƙasƙantar da mai girman kai  
za a kuma lalatar da fariyar masu ɗaga kai;  
Ubangiji kaɗai za a ɗaukaka a wannan rana.   
   
 
12 Ubangiji Maɗaukaki yana da rana ajiye  
domin dukan masu girman kai da masu fariya  
domin dukan waɗanda aka ɗaukaka  
(zai kuwa ƙasƙantar da su),   
13 domin dukan al’ul na Lebanon, masu tsayi da masu fariya,  
da kuma dukan itatuwan oak na Bashan,   
14 domin dukan dogayen duwatsu  
da kuma tuddai masu tsayi,   
15 domin kowace doguwar hasumiya  
da kowace katanga mai ƙarfi,   
16 domin kowane jirgin ruwan kasuwanci  
da kuma jirgi mafi girma mafi kyau.   
17 Za a jawo mai girman kai ƙasa  
a kuma ƙasƙantar da mai ɗaga kai;  
Ubangiji kaɗai za a ɗaukaka a wannan rana,   
18 za a kuma kawar da gumaka ƙaƙaf.   
   
 
19 Mutane za su gudu zuwa kogwannin duwatsu  
da kuma ramummuka a ƙasa  
daga razanar Ubangiji  
da kuma darajar ɗaukakarsa,  
sa’ad da ya tashi don yă girgiza duniya.   
20 A wannan rana mutane za su zubar wa  
jaba da jamage  
gumakansu na azurfa da gumakansu na zinariya  
da suka yi don su bauta musu.   
21 Za su gudu zuwa kogwannin duwatsu  
da kuma zuwa tsagaggun duwatsu  
daga razanar Ubangiji  
da kuma darajar ɗaukakarsa,  
sa’ad da ya tashi don yă girgiza duniya.   
   
 
22 Ku daina dogara ga mutum,  
wanda numfashi ne kawai yake da shi a hancinsa.  
Wace daraja gare shi?