11
Reshe daga Yesse
Toho zai fito daga kututturen Yesse;
daga saiwarsa Reshe zai ba da ’ya’ya.
Ruhun Ubangiji zai kasance a kansa,
Ruhun hikima da na fahimta,
Ruhun shawara da na iko,
Ruhun sani da na tsoron Ubangiji,
zai kuwa ji daɗin tsoron Ubangiji.
 
Ba zai yi hukunci ta wurin abin da ya gani da idanunsa ba,
ba zai kuwa yanke shawara ta wurin abin da ya ji da kunnuwansa ba;
amma da adalci zai yi wa masu bukata shari’a,
da gaskiya zai yanke shawarwari saboda matalautan duniya.
Kamar sanda zai bugi duniya da maganar bakinsa;
da numfashin leɓunansa zai yanke mugaye.
Adalci ne zai zama abin ɗamararsa
aminci kuma igiyar da zai ɗaura kewaye da gindinsa.
 
Kyarkeci zai zauna tare da ɗan rago
damisa za tă kwanta tare da akuya,
ɗan maraƙi da zaki da ɗan saniya za su yi kiwo tare;
ɗan yaro ne zai lura da su.
Saniya da beyar za su yi kiwo tare,
ƙananansu za su kwanta tare,
zaki kuma zai ci ciyawa kamar saniya.
Jariri zai yi wasa kurkusa da ramin gamsheƙa,
ɗan yaro kuma zai sa hannunsa a ramin maciji mai mugun dafi.
Ba za su yi lahani ko su hallaka
wani a dutsena mai tsarki ba,
gama duniya za tă cika da sanin Ubangiji
kamar yadda ruwaye suka rufe teku.
10 A wannan rana Saiwar Yesse zai miƙe kamar tuta don mutanenta; al’ummai za su tattaru wurinsa, wurin hutunsa kuma zai zama mai daraja. 11 A wannan rana Ubangiji zai miƙa hannunsa sau na biyu don yă maido da raguwar da ta rage na mutanensa daga Assuriya, daga Masar ta Ƙasa, daga Masar ta Bisa,* daga Kush, daga Elam, daga Babiloniya, daga Hamat da kuma daga tsibiran teku.
12 Zai tā da tuta saboda al’ummai
yă kuma tattara masu zaman bauta na Isra’ila;
zai tattara mutanen Yahuda da suke a warwatse
kusurwoyi huɗu na duniya.
13 Kishin Efraim zai ɓace,
za a kuma kau da abokan gāban Yahuda;
Efraim ba zai yi kishin Yahuda ba,
haka ma Yahuda ba zai yi gāba da Efraim ba.
14 Tare za su fāɗa wa Filistiyawa da yaƙi daga yamma;
tare za su washe mutane wajen gabas.
Za su ɗibiya hannuwa a kan Edom da Mowab,
Ammonawa kuma za su yi musu biyayya.
15  Ubangiji zai busar da
bakin tekun Masar;
da iska mai zafi zai share hannunsa
a bisa Kogin Yuferites§
Zai rarraba shi yă zama ƙanana rafuffuka bakwai
saboda mutane su iya hayewa da ƙafa.
16 Za a yi babbar hanya saboda raguwa mutanensa
da ta rage daga Assuriya,
kamar yadda ta kasance wa Isra’ila
sa’ad da suka fito daga Masar.
* 11:11 Da Ibraniyanci daga Faturos 11:11 Wato, yankin Nilu na Bisa 11:11 Da Ibraniyanci Shinar § 11:15 Da Ibraniyanci Kogi