4
Tuhuma a kan Isra’ila
Ku ji maganar Ubangiji, ku Isra’ilawa,
gama Ubangiji yana da tuhumar da zai kawo
a kan ku waɗanda suke zama a ƙasar.
“Babu aminci, babu ƙauna,
babu yarda da Allah a cikin ƙasar.
Akwai la’ana ce kawai,* yin ƙarya da kisa,
yin sata da zina;
sun wuce gona da iri,
kisankai a kan kisankai.
Saboda wannan ƙasar tana makoki,
kuma dukan waɗanda suke zama a cikinta sun lalace;
namun jeji da tsuntsayen sararin sama
da kuma kifin teku suna mutuwa.
 
“Amma kada wani mutum yă kawo tuhuma,
kada wani mutum yă zargi wani,
gama mutanenka suna kama da waɗanda
suke kawo tuhume-tuhume a kan firist ne.
Kuna tuntuɓe dare da rana,
annabawa ma suna tuntuɓe tare da ku.
Saboda haka zan hallaka mahaifiyarku,
mutanena suna hallaka saboda jahilci.
 
“Domin kun ƙi neman sani,
ni ma na ƙi ku a matsayin firistocina;
domin kun ƙyale dokar Allahnku,
ni ma zan ƙyale ’ya’yanku.
Yawan ƙaruwar firistoci,
haka suke yawan zunubi a kaina;
sun yi musaya Ɗaukakarsu da wani abin kunya.
Suna ciyar da kansu a kan zunuban mutanena
suna kuma haɗamar muguntarsu.
Zai kuwa zama, kamar yadda mutane suke, haka firistoci suke.
Zan hukunta dukansu saboda al’amuransu
in kuma sāka musu saboda ayyukansu.
 
10 “Za su ci amma ba za su ƙoshi ba;
za su shiga karuwanci amma ba za su ƙaru ba,
gama sun rabu da Ubangiji
don su ba da kansu 11 ga karuwanci,
ga tsoho da kuma sabon ruwan inabi,
waɗanda suka ɗauke ganewar mutanena.
12 Sun nemi shawarar gunkin da aka yi da itace
suka kuwa sami amsa daga sanda.
Halin karuwanci yakan ɓad da su;
sun yi rashin aminci ga Allahnsu.
13 Suna miƙa hadaya a kan ƙwanƙolin duwatsu
suna kuma ƙone hadayu a kan tuddai,
a ƙarƙashin itatuwa oak, aduruku da katambiri,
inda inuwa take da daɗi.
Saboda haka ’ya’yanku mata suka juya wa karuwanci
surukanku mata kuma suka shiga yin zina.
 
14 “Ba zan hukunta ’ya’yanku mata
sa’ad da suka juya ga yin karuwanci ba,
balle surukanku mata,
sa’ad da suka yi zina,
gama mazan da kansu suna ma’amala da karuwai
suna kuma miƙa hadaya tare da karuwai na masujada,
mutane marasa ganewa za su lalace!
 
15 “Ko da yake kun yi zina, ya Isra’ila,
kada Yahuda ya yi laifi.
 
“Kada ku tafi Gilgal;
kada ku haura zuwa Bet-Awen.
Kuma kada ku rantse cewa, ‘Muddin Ubangiji yana a raye!’
16 Isra’ilawa masu taurinkai ne,
kamar karsana mai taurinkai.
Yaya Ubangiji zai iya kiwonsu
kamar tumaki a makiyaya mai ɗanyar ciyawa?
17 Efraim ya haɗa kai da gumaka;
ku ƙyale shi kurum!
18 Ko ma sa’ad da abin shansu ya ƙare,
sai suka ci gaba da karuwancinsu;
masu mulkinsu suna ƙaunar abin kunya.
19 Guguwa za tă share su,
hadayunsu kuma za su jawo musu abin kunya.
* 4:2 Wato, a yi la’ana a kai 4:3 Ko kuwa ta bushe 4:15 Bet-Awen yana nufin gidan mugunta (sunan Betel, wanda yake nufin gidan Allah).