36
Zuriyar Isuwa
Waɗannan su ne zuriyar Isuwa (wato, Edom).
 
Isuwa ya ɗauko matansa daga cikin matan Kan’ana, ya ɗauko Ada ’yar Elon mutumin Hitti, da Oholibama ’yar Ana wadda take jikanyar Zibeyon Bahiwiye ya kuma auri Basemat ’yar Ishmayel wadda take ’yar’uwar Nebayiwot.
Ada ta haifi wa Isuwa, Elifaz. Basemat kuma ta haifa masa Reyuwel. Oholibama kuwa ta haifa masa Yewush, Yalam da Kora. Waɗannan su ne ’ya’yan Isuwa maza, waɗanda aka haifa masa a Kan’ana.
Isuwa ya ɗauki matansa da ’ya’yansa maza da mata da kuma dukan membobin gidansa, ya kuma ɗauki shanunsa da dukan sauran dabbobinsa, da dukan dukiyarsa da ya samu a ƙasar Kan’ana zuwa wata ƙasa nesa da ɗan’uwansa Yaƙub. Mallakarsu ta yi yawa ƙwarai da ba za su iya zauna tare ba; gama ƙasar da suke zaune a ciki ba za tă ishe su su biyu ba saboda dabbobinsu. Saboda haka Isuwa (wato, Edom) ya zauna a ƙasar tuddai na Seyir.
 
Wannan shi ne zuriyar Isuwa, kakan mutanen Edom, a ƙasar tuddai na Seyir.
 
10 Waɗannan su ne sunayen ’ya’yan Isuwa maza,
Elifaz, ɗan Ada matar Isuwa, da Reyuwel ɗan Basemat matar Isuwa.
11 ’Ya’yan Elifaz maza su ne,
Teman, Omar, Zefo, Gatam da Kenaz. 12 Elifaz ɗan Isuwa kuma yana da ƙwarƙwara mai suna Timna, wadda ta haifa masa Amalek. Waɗannan su ne jikokin Ada matar Isuwa.
13 ’Ya’yan Reyuwel maza su ne,
Nahat, Zera, Shamma da Mizza. Waɗannan su ne jikokin Basemat matar Isuwa.
14 ’Ya’yan Oholibama maza ’yar Ana wadda take jikanyar Zibeyon, matar Isuwa, waɗanda ta haifa wa Isuwa su ne,
Yewush, Yalam da Kora.
 
15 Waɗannan su ne manya a cikin zuriyar Isuwa,
’Ya’ya Elifaz maza ɗan farin Isuwa,
Shugabannin su ne; Teman, Omar, Zefo, Kenaz, 16 Kora,* Gatam da kuma Amalek. Waɗannan ne manya da suka fito daga dangin Elifaz a Edom; su ne jikokin Ada.
17 ’Ya’yan Reyuwel maza,
Shugabannin su ne; Nahat, Zera, Shamma da Mizza. Waɗannan su ne manya da suka fito daga dangin Reyuwel a Edom; su ne jikokin Basemat matar Isuwa.
18 ’Ya’yan Oholibama maza matar Isuwa,
Shugabannin su ne; Yewush, Yalam da Kora. Waɗannan su ne manya da suka fito daga dangin Oholibama ’yar Ana matar Isuwa.
19 Waɗannan su ne ’ya’yan Isuwa maza (wato, Edom), waɗannan ne manyansu.
 
20 Waɗannan su ne ’ya’yan Seyir Bahore maza, waɗanda suke zaune a yankin,
Lotan, Shobal, Zibeyon, Ana, 21 Dishon, Ezer da Dishan. Waɗannan su ne manyan Horiyawa, ’ya’yan Seyir, maza, a ƙasar Edom.
22 ’Ya’yan Lotan maza su ne,
Hori da Homam. Timna ’yar’uwar Lotan ce.
23 ’Ya’yan Shobal maza su ne,
Alwan, Manahat, Ebal, Shefo da Onam.
24 ’Ya’yan Zibeyon maza su ne,
Aiya da Ana. Wannan shi ne Ana wanda ya sami maɓulɓulan ruwan zafi a hamada yayinda yake kiwon jakuna na mahaifinsa Zibeyon.
25 ’Ya’yan Ana su ne,
Dishon da Oholibama ’yar Ana.
26 ’Ya’yan Dishon maza§ su ne,
Hemdan, Eshban, Itran da Keran.
27 ’Ya’yan Ezer maza su ne,
Bilhan, Za’aban da Akan.
28 ’Ya’yan Dishan maza su ne,
Uz da Aran.
29 Waɗannan su ne manyan Horiyawa,
Lotan, Shobal, Zibeyon, Ana, 30 Dishon, Ezer da Dishan.
Waɗannan su ne manyan Horiyawa, bisa ga ɓangarorinsu, a ƙasar Seyir.
Masu mulkin Edom
31 Waɗannan su ne sarakunan da suka yi mulki a Edom kafin wani sarki mutumin Isra’ila yă yi mulki,*
32 Bela ɗan Beyor ya zama sarkin Edom. Sunan birninsa shi ne Dinhaba.
33 Sa’ad da Bela ya rasu, Yobab ɗan Zera daga Bozra ya gāje shi.
34 Sa’ad da Yobab ya rasu, Husham daga ƙasar Temaniyawa ya gāje shi.
35 Sa’ad da Husham ya rasu, Hadad ɗan Bedad, wanda ya ci Midiyan da yaƙi a ƙasar Mowab, ya gāje shi. Sunan birninsa shi ne Awit.
36 Sa’ad da Hadad ya rasu, Samla daga Masreka ya gāje shi.
37 Sa’ad da Samla ya rasu, Sha’ul daga Rehobot na ta kogi ya gāje shi.
38 Sa’ad da Sha’ul ya rasu, Ba’al-Hanan ɗan Akbor ya gāje shi.
39 Sa’ad da Ba’al-Hanan ɗan Akbor ya rasu, Hadad ya gāje shi. Sunan birninsa shi ne Fau, kuma sunan matarsa Mehetabel ce ’yar Matired, jikanyar Me-Zahab.
 
40 Waɗannan su ne manya da suka fito daga zuriyar Isuwa, bisa ga danginsu, bisa kuma ga kabilansu da yankunansu. Sunayensu su ne,
Timna, Alwa, Yetet.
41 Oholibama, Ela, Finon.
42 Kenaz, Teman, Mibzar.
43 Magdiyel da Iram.
Waɗannan su ne manyan Edom bisa ga mazauninsu cikin ƙasar da suka zauna.
 
Wannan shi ne zuriyar Isuwa, kakan mutanen Edom.
* 36:16 Masoretik, Fentatut na Samariya (dubi kuma Far 36.11 da 2Tar 1.3-6) ba su da Kora. 36:22 Da Ibraniyanci Hemam, wani suna na Homam (dubi 1Tar 1.39) 36:24 Bulget, Siriyak sami ruwa; ma’anar Ibraniyanci don wannan kalma ba tabbatacce ba ne. § 36:26 Da Ibraniyanci Dishan, wani suna na Dishon * 36:31 Ko kuwa kafin wani sarkin Isra’ilawa ya yi mulki a kansu 36:37 Mai yiwuwa Yuferites 36:39 Yawancin rubuce-rubucen hannu na Masoretik, Fentatut na Samariya da Siriyak (dubi kuma 1Tar 1.50); yawancin rubuce-rubucen hannu na Masoretik suna da Hadar ne.