10
Tsarin Al’ummai
1 Wannan shi ne labarin Shem, Ham da Yafet, ’ya’yan Nuhu maza, waɗanda su ma sun haifi ’ya’ya maza bayan ambaliyar.
Mutanen Yafet
2 ’Ya’yan Yafet maza su ne,
Gomer, Magog, Madai da Yaban, Tubal, Meshek, da kuma Tiras.
3 ’Ya’yan Gomer maza su ne,
Ashkenaz, Rifat, da Togarma.
4 ’Ya’yan maza Yaban su ne,
Elisha, Tarshish, Kittim da Rodanim.
5 (Daga waɗannan mutane ne masu zama a bakin teku suka bazu zuwa cikin ƙasashensu da kuma cikin al’ummansu, kowanne da yarensa.)
Mutanen Ham
6 ’Ya’yan Ham maza su ne,
Kush, Masar, Fut, da Kan’ana.
7 ’Ya’yan Kush maza su ne,
Seba, Hawila, Sabta, Ra’ama da Sabteka.
’Ya’yan Ra’ama maza kuwa su ne,
Sheba da Dedan.
8 Kush shi ne mahaifin Nimrod wanda ya yi girma ya zama jarumin yaƙi a duniya.
9 Shi babban maharbi ne a gaban Ubangiji. Shi ya sa akan ce, kamar Nimrod babban maharbi a gaban Ubangiji.
10 Cibiyoyin mulkinsa na farko su ne Babilon, Erek, Akkad, da Kalne a cikin Shinar.
11 Daga wannan ƙasa, sai ya tafi Assuriya, inda ya gina Ninebe, Rehobot Ir, Kala
12 da Resen, wadda take tsakanin Ninebe da Kala; wanda yake babban birni.
13 Mizrayim shi ne mahaifin
Ludiyawa, Anamawa, Lehabiyawa, Naftuhiyawa,
14 Fetrusiyawa, da Kasluhiyawa (inda Filistiyawa suka fito) da kuma Kaftorawa.
15 Kan’ana shi ne mahaifin,
Sidon ɗan farinsa, da na Hittiyawa,
16 Yebusiyawa, Amoriyawa, Girgashiyawa,
17 Hiwiyawa, Arkiyawa, Siniyawa,
18 Arbadiyawa, Zemarawa, da Hamawa.
Daga baya zuriyar Kan’aniyawa suka yaɗu
19 har iyakar Kan’ana ta kai Sidon ta wajen Gerar har zuwa Gaza, sa’an nan ta milla zuwa Sodom, Gomorra, Adma da Zeboyim, har zuwa Lasha.
20 Waɗannan su ne ’ya’yan Ham maza bisa ga zuriyarsu da yarurrukansu, cikin ƙasashensu da kuma al’ummominsu.
Mutanen Shem
21 Aka kuma haifa wa Shem, wan Yafet, ’ya’ya maza. Shem shi ne kakan ’ya’yan Eber duka.
22 ’Ya’yan Shem maza su ne,
Elam, Asshur, Arfakshad, Lud da Aram.
23 ’Ya’yan Aram maza su ne,
Uz, Hul, Geter da Mash.
24 Arfakshad ne mahaifin Shela.
Shela kuma shi ne mahaifin Eber.
25 Aka haifa wa Eber ’ya’ya maza biyu.
Aka ba wa ɗaya suna Feleg, gama a zamaninsa ne aka raba duniya; aka kuma sa wa ɗan’uwansa suna Yoktan.
26 Yoktan shi ne mahaifin,
Almodad, Shelef, Hazarmawet, Yera,
27 Hadoram, Uzal, Dikla,
28 Obal, Abimayel, Sheba,
29 Ofir, Hawila da Yobab. Dukan waɗannan ’ya’yan Yoktan maza ne.
30 Yankin da suka zauna ya miƙe daga Mesha zuwa wajen Sefar a gabashin ƙasar tudu.
31 Waɗannan su ne ’ya’yan Shem maza bisa ga zuriyarsu da yarurrukansu, cikin ƙasashensu da kuma al’ummominsu.
32 Waɗannan su ne zuriyar ’ya’yan Nuhu maza bisa ga jerin zuriyarsu cikin al’ummominsu. Daga waɗannan ne al’ummomi suka bazu ko’ina a duniya bayan ambaliya.