2
Manzanni sun karɓi Bulus
Bayan shekara goma sha huɗu sai na sāke haurawa zuwa Urushalima, a wannan lokaci na tafi tare da Barnabas. Na kuma ɗauki Titus muka tafi tare. Na tafi ne bisa ga wani wahayi. Da na kai can, sai na bayyana musu bisharar da nake wa’azi a cikin Al’ummai. Na yi haka a keɓance a gaban waɗanda suke shugabanni, don tsoro kada gudun da nake yi, ko kuwa na riga na yi, yă zama a banza. Amma ko Titus ma da yake tare da ni, ba a ce dole sai ya yi kaciya ba, ko da yake shi mutumin Al’ummai ne. Wannan zancen kaciya ya taso domin waɗansu ’yan’uwan ƙarya sun shiga cikinmu domin su yi leƙe a kan ’yancin da muke da shi a cikin Kiristi Yesu, su kuma mai da mu bayi. Ba mu kuwa ba su zarafi ba ko kaɗan, don gaskiyar bishara ta ci gaba da kasance tare da ku.
Game da waɗanda aka ɗauka a dā a kan su wani abu ne, ko wane ne su, duk ɗaya ne a wurina; gama Allah ba ya nuna bambanci, ina dai gaya muku waɗannan da suke wani abu ne a dā, ba su ƙara mini kome ba. A maimakon haka, sun ga cewa an danƙa mini hakkin wa’azin bishara ga Al’ummai,* kamar yadda aka danƙa wa Bitrus ga Yahudawa. Gama Allah wanda ya yi aiki a cikin hidimar Bitrus a matsayin manzo ga Yahudawa, haka ma ya yi aiki a cikin hidimata a matsayin manzo ga Al’ummai. Yaƙub, Bitrus da Yohanna waɗanda suke fitattun ginshiƙai, sun karɓe ni da Barnabas da hannu biyu biyu sa’ad da suka gane alherin da aka ba ni. Suka kuma yarda cewa ya kamata mu tafi wajen Al’ummai, su kuwa su tafi wajen Yahudawa. 10 Abin da dai suka roƙa shi ne ya kamata mu riƙa tuna da matalauta, abin nan da nake marmarin yi.
Bulus ya tsawata wa Bitrus
11 Sa’ad da Bitrus ya zo Antiyok, na tsawata masa ido da ido don laifinsa a fili yake. 12 Kafin waɗansu mutane su zo daga wurin Yaƙub, yakan ci abinci tare da Al’ummai. Amma da suka iso, sai ya fara janyewa, ya kuma ware kansa daga wajen Al’ummai domin yana tsoron waɗanda suke ƙungiyar masu kaciya. 13 Sauran Yahudawa suka haɗa kai da shi a munafuncinsa har Barnabas ma ya bauɗe.
14 Da na ga cewa ba sa yin daidai da gaskiyar bishara, sai na ce wa Bitrus a gabansu duka, “Kai mutumin Yahuda ne, duk da haka kana rayuwa kamar Ba’al’umme ba kamar mutumin Yahuda ba. To, yaya aka yi, kana tilasta Al’ummai su bi al’adun Yahudawa?
15 “Mu da muke Yahudawa ta wurin haihuwa ba Al’ummai masu zunubi ba, 16 mun san cewa mutum ba ya samun kuɓuta ta wurin kiyaye Doka, sai dai ta wurin bangaskiya cikin Kiristi Yesu. Saboda haka, mu ma, muka sa bangaskiyarmu cikin Kiristi Yesu don mu sami kuɓuta ta wurin bangaskiya cikin Kiristi ba ta wurin kiyaye Doka ba, domin ba wanda zai kuɓuta ta wurin bin Doka.
17 “In kuwa ya zama muna so mu sami zaman marasa laifi a gaban Allah ta wurin dogara ga Kiristi, sa’an nan an same mu mu kanmu ma masu zunubi ne, ashe, ko wannan zai nuna Kiristi yana ƙarfafa zunubi ke nan? A’a, ko kusa! 18 In na sāke gina abin da na rushe, na zama mai karyar Doka ke nan.
19 “Gama ta wurin Doka na mutu ga Doka saboda in rayu ga Allah. 20 An gicciye ni tare da Kiristi. Yanzu ba ni ne nake raye ba, Kiristi ne yake raye a cikina. Rayuwar da nake yi a jiki, ina rayuwa ce ta wurin bangaskiya cikin Ɗan Allah, wanda ya ƙaunace ni ya kuma ba da kansa domina. 21 Ba na ajiyar alherin Allah a gefe, gama da a ce ana samun adalci ta wurin Doka, ai, da Kiristi ya mutu a banza ke nan!”
* 2:7 Girik marasa kaciya 2:7 Girik masu kaciya; haka ma a ayoyi 8 da kuma 9