9
Addu’ar Ezra game da auratayya
Bayan an yi waɗannan abubuwa duka, sai shugabanni suka zo wurina suka ce, “Mutanen Isra’ila, har da firistoci da Lawiyawa ba su keɓe kansu daga maƙwabtansu ba, ba su kuma keɓe kansu daga irin rayuwar ƙazantar mutanen ƙasar ba, wato, rayuwar irinta Kan’aniyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Yebusiyawa, da Ammonawa, da Mowabawa, da Masarawa da Amoriyawa. Sun auro wa kansu da ’ya’yansu ’yan mata mutanen nan, ta haka aka kwaɓa zuriyar da aka tsarkake da ta mutanen nan da suke tare da su. Shugabanni da manyan ma’aikata su ne a gaba-gaba a aikata wannan abin kunya.”
Sa’ad da na ji wannan, sai na yaga rigata da alkyabbata, na tsittsige gashin kaina da na gemuna, na zauna, na rasa abin da yake mini daɗi. Sai duk waɗanda suke tsoron maganar Allah na Isra’ila suka kewaye ni don su ji wannan rashin imani wanda waɗanda suka dawo bauta suka yi. Na kuwa zauna a can a rikice, har lokacin miƙa hadaya na yamma.
Sa’an nan a lokacin miƙa hadaya na yamma, na tashi da ɓacin raina, da yagaggun kayana, na durƙusa na miƙa hannuwana sama ga Ubangiji Allahna na kuma yi addu’a, na ce,
“Ya Allah, ina cike da kunya, ba zan iya ɗaga fuskata gare ka ba, ya Allahna, domin zunubanmu sun fi mu tsayi, tudunsu har ya kai sama. Tun daga zamanin kakanninmu har zuwa yanzu, zunubanmu suna da yawa. Domin zunubanmu, mu da sarakunanmu, da firistocinmu aka kama mu, aka wulaƙanta mu, muka zama bayi a hannun sarakuna waɗansu ƙasashe.
“Amma a yanzu a wannan ɗan lokaci Ubangiji Allahnmu ya yi mana jinƙai, ya bar mana saura, ya kuma ba mu wuri a wurinsa mai tsarki, ya kuma ba mu ganin haske, ya ɗan rage mana nauyin bauta. Ko da yake mu bayi ne, Allahnmu bai yashe mu cikin daurin talala da muke ciki ba, ya sa sarakunan Farisa suka yi mana kirki. Ya ba mu sabuwar dama don mu sāke gina haikalin Allahnmu, mu kuma gyara katangar, ya kuma ba mu kāriya a Yahuda da Urushalima.
10 “Amma yanzu, ya Allahnmu, me za mu ce game da wannan? Gama mun ƙi bin 11 dokokin da ka bayar ta wurin annabawa lokacin da ka ce, ‘Ƙasar da za ku mallaka, ƙasa ce marar tsarki, mutanenta sun ɓata ta da ƙazamin hali, ƙazamin halinsu ya ɓata ko’ina. 12 Saboda haka kada ku aurar musu da ’yan matanku, kada kuma ku auro wa ’ya’yanku maza ’yan matansu. Kada ku yi wata yarjejjeniya ta abokantaka da su. Idan kun yi biyayya za ku yi ƙarfi, ku kuma ci albarkar ƙasar, har ku bar wa ’ya’yanku gādo na har abada.’
13 “Abubuwan nan sun faru da mu sakamakon mugayen ayyukanmu ne, amma duk da haka ya Allahnmu, ba ka ba mu horo bisa ga yawan zunubanmu ba, ka kuma bar mana saura. 14 Za mu sāke ƙin yin biyayya da umarninka mu yi auratayya da mutanen nan da suke aikata waɗannan abubuwan banƙyama? Ba za ka yi fushi da mu, ka ƙone mu da fushinka har babu ɗan saura ba? 15 Ya Ubangiji Allah na Isra’ila, kai mai adalci ne! Yau an bar mu da sauran da ya tsira. Ga mu nan a gabanka masu zunubi, gama ba wanda zai iya tsayawa a gabanka.”