5
1 “Yanzu, ɗan mutum, ka ɗauki takobi mai kaifi ka kuma yi amfani da shi kamar rezan mai aski don askin kanka da gemunka. Sa’an nan ka ɗauki ma’auni ka kuma raba gashin.
2 Sa’ad da kwanakin ƙawanyarka sun ƙare, sai ka ƙone kashi ɗaya bisa uku na gashin da wuta a cikin birnin. Ka ɗauki kashi ɗaya bisa uku ka yayyanka shi da takobi kewaye da birnin. Ka kuma watsar da kashi ɗaya bisa uku a iska. Gama zan fafare su da takobin da aka zāre.
3 Amma ka ɗibi gashi kaɗan ka daure a shafin rigarka.
4 Har yanzu, ka ɗibi kaɗan na waɗannan ka zuba su cikin wuta su kuma ƙone. Wuta zai bazu daga nan zuwa dukan gidan Isra’ila.
5 “Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce Urushalima ce wannan, wadda na kafa a tsakiyar al’ummai, da ƙasashe kewaye da ita a ko’ina.
6 Duk da haka cikin muguntarta ta yi tayarwa a kan dokokina da ƙa’idodina fiye da al’ummai da ƙasashe kewaye da ita. Ta ƙi dokokina ba tă kuwa bi ƙa’idodina ba.
7 “Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce kin yi ƙin ji fiye da al’umman da suke kewaye da ke ba ki kuma bi ƙa’idodina ko ki kiyaye dokokina ba. Ba ki ma dace da matsayin al’umman da suke kewaye da ke ba.
8 “Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce Ni kaina ina gāba da ke, Urushalima, kuma zan hukunta ki a gaban al’ummai.
9 Saboda dukan gumakan banƙyamarki, zan yi abin da ban taɓa yi ba, ba kuwa zan ƙara yinsa ba.
10 Saboda haka a cikinki ubanni za su ci ’ya’yansu, ’ya’ya kuma za su ci ubanninsu. Zan hukunta ki zan kuma watsar da dukan waɗanda suke tsira da suke naki a iska.
11 Saboda haka muddin ina a raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, domin kin ƙazantar da wuri mai tsarkina da dukan mugayen siffofinki da kuma ayyukanki masu banƙyama, ni kaina zan janye alherina; ba zan ji tausayinki ko in haƙura da ke ba.
12 Kashi ɗaya bisa uku na mutanenki za su mutu da annoba ko su mutu da yunwa a cikinki; kashi ɗaya bisa uku takobi ne zai kashe su a waje da katangarki; kashi ɗaya bisa uku kuma zan watsar a iska in kuma fafare su da takobin da aka zāre.
13 “Sa’an nan ne fushina zai huce hasalata a kanki kuma ta lafa, in kuma wartsake. Kuma sa’ad da na zuba fushina a kansu, a sa’an nan ne za su san cewa Ni Ubangiji na yi magana a cikin fushin kishina a kansu.
14 “Zan mai da ki kufai da kuma abin dariya a cikin al’ummai kewaye da ke, a gaban dukan waɗanda suke wucewa.
15 Za ki zama abin dariya da abin ba’a, kashedi da abin banrazana ga al’ummai kewaye da ke sa’ad da na hukunta ki cikin fushi da cikin hasala da kuma tsawatawa mai zafi. Ni Ubangiji na faɗa.
16 Sa’ad da na harbe ki da mugayen kibiyoyina da kuma kibiyoyi masu hallakarwa na yunwa, zan yi harbi don in kashe ki. Zan kawo ƙarin yunwa a kanki in kuma yanke tanadin abincinki.
17 Zan aika da yunwa da namun jeji a kanki, za su kuma bar ku ba ’ya’ya. Annoba da zub da jini za su ratsa cikinki, zan kuma kawo takobi a kanki. Ni Ubangiji na faɗa.”