35
Annabci a kan Edom
1 Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
2 “Ɗan mutum, ka fuskanci Dutsen Seyir; ka yi annabci a kansa
3 ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gāba da kai, Dutsen Seyir, zan kuma miƙa hannuna gāba da kai in mai da kai kango.
4 Zan mai da garuruwanka kufai za ka kuma zama kango. Sa’an nan za ka san cewa ni ne Ubangiji.
5 “ ‘Domin ka riƙe ƙiyayya ta tun dā, ka kuma ba da mutanen Isra’ila domin a kashe su da takobi a lokacin masifarsu, lokacin da adadin horonsu ya cika,
6 saboda haka muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, zan sa a zub da jininka zan kuwa fafare ka. Da yake ba ka ƙi zub da jini ba, zub da jini zai fafare ka.
7 Zan mai da Dutsen Seyir kango in kuma yanke dukan waɗanda suke shiga da fita a cikinka.
8 Zan cika duwatsunka da matattu; waɗanda aka kashe da takobi za su fāɗi a kan tuddanka, da cikin kwarurukanka, da cikin dukan kwazazzabanka.
9 Zan mai da kai kango har abada; ba za a zauna a cikin garuruwanka ba. Sa’an nan za ka san cewa ni ne Ubangiji.
10 “ ‘Domin kun ce, “Waɗannan al’ummai biyu da ƙasashe za su zama namu za mu kuma mallake su,” ko da yake Ni Ubangiji ina a can,
11 saboda haka muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, zan sāka maka gwargwadon fushi da kuma kishin da ka nuna a ƙiyayyarsu da ka yi zan kuma sanar da kaina a cikinsu sa’ad da na hukunta ka.
12 Sa’an nan za ka san cewa Ni Ubangiji na ji duk abubuwan banzan da ka faɗa a kan duwatsun Isra’ila. Ka ce, “An mai da su kango an kuma ba mu su mu cinye.”
13 Ka yi fariya a kaina, ka kuma yi magana a kaina ba gaggautawa, na ji shi sarai.
14 Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa yayinda dukan duniya take farin ciki, zan mai da kai kango.
15 Domin ka yi farin ciki sa’ad da gādon gidan Isra’ila ya zama kufai, haka zan yi da kai, ya Dutsen Seyir, kai da dukan Edom. Sa’an nan za ka san cewa ni ne Ubangiji.’ ”