18
Mutumin da ya yi zunubi zai mutu
1 Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
2 “Me ku mutane kuke nufi da faɗar wannan karin magana a kan ƙasar Isra’ila cewa,
“ ‘Ubanni sun ci ’ya’yan inabi masu tsami,
haƙoran ’ya’ya kuwa sun mutu’?
3 “Muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, ba za ku ƙara faɗar wannan karin magana a Isra’ila ba.
4 Gama kowane mai rai nawa ne, mahaifi da ɗa, duk nawa ne. Mutumin da ya yi zunubi shi zai mutu.
5 “A ce akwai mai adalci
wanda yake aikata abin da yake daidai da kuma gaskiya;
6 ba ya cin abinci a duwatsun tsafi
ko ya dogara ga gumakan gidan Isra’ila.
Ba ya ƙazantar da matar maƙwabcinsa
ko ya kwana da mace lokacin al’adarta ba.
7 Ba ya cin zalin wani,
amma yakan mayar wa wanda ya ba shi jingina abin da ya jinginar masa.
Ba ya yi fashi
amma yakan ba wa mayunwata abinci
ya kuma tanada wa marasa tufafi riga.
8 Ba ya ba da bashi da ruwa
ko ya karɓa ƙarin riba.
Yakan janye hannunsa daga aikata mugunta
yakan kuma yi shari’a cikin gaskiya tsakanin mutum da mutum.
9 Yana bin ƙa’idodina
yana kuma kiyaye dokokina da aminci.
Wannan mutumin adali ne;
tabbatacce zai rayu,
in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
10 “A ce yana da ɗa wanda yana kisa ko yana yin ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa
11 (ko da yake mahaifin bai yi ko ɗaya daga cikinsu ba).
“Yakan ci abinci a duwatsun tsafi.
Yakan ƙazantar da matar maƙwabci.
12 Yakan ci zalin matalauta da mabukata.
Yakan yi fashi.
Ba ya mayar da abin da aka jinginar masa.
Ya dogara ga gumaka.
Yana aikata ayyukan banƙyama.
13 Yakan ba da bashi da ruwa ya kuma karɓi riba mai yawa.
Irin wannan mutum zai rayu? Ba zai rayu ba! Domin ya aikata dukan waɗannan abubuwa masu banƙyama, tabbatacce za a kashe shi, kuma hakkin jininsa zai zauna a kansa.
14 “Amma a ce wannan ɗa yana da ɗa wanda ya ga dukan zunuban da mahaifinsa yake aikata, kuma ko da yake ya gan su, bai yi ko ɗaya daga cikin irin abubuwan nan ba, wato,
15 “Bai ci abinci a duwatsun tsafi ba
ko ya dogara ga gumakan gidan Isra’ila.
Bai ƙazantar da matar maƙwabcinsa ba.
16 Bai ci zalin wani
ko ya karɓi jingina ba.
Ba ya fashi
amma yakan ba da abincinsa ga mayunwata
ya tanada tufafi wa marasa tufafi.
17 Yakan janye hannunsa daga zunubi
ba ya kuma ba da bashi da ruwa ko karɓan riba da yawa.
Yakan kiyaye dokokina ya kuma bi ƙa’idodina.
Ba zai mutu saboda zunubin mahaifinsa ba; tabbatacce zai rayu.
18 Amma mahaifinsa zai mutu saboda zunubinsa, domin ya yi ƙwace, ya yi wa ɗan’uwansa fashi ya kuma yi abin da ba daidai ba a cikin mutanensa.
19 “Duk da haka kukan yi tambaya, ‘Me ya sa ɗan ba zai sami rabo a laifin mahaifinsa ba?’ Da yake ɗan ya yi abin da yake daidai da kuma gaskiya, ya kuma kiyaye dukan ƙa’idodina, tabbatacce zai rayu.
20 Mutumin da ya yi zunubi shi zai mutu. Ɗa ba zai sami rabo a laifin mahaifi ba, mahaifi ba zai sami rabo a laifi ɗa ba. Adalcin adali zai zama nasa, muguntar mugu za tă koma kansa.
21 “Amma in mugun mutum ya juya daga dukan zunubin da ya aikata ya kuma kiyaye dukan ƙa’idodina ya kuwa yi abin da yake daidai da kuma gaskiya, tabbatacce zai rayu; ba zai mutu ba.
22 Babu laifin da ya yi da za a tuna da su. Saboda abubuwan adalcin da ya aikata, zai rayu.
23 Ina jin daɗin mutuwar mugu ne? In ji Ubangiji Mai Iko Duka. A maimako, ban fi jin daɗi sa’ad da suka juyo daga hanyoyinsu suka rayu ba?
24 “Amma in mai adalci ya juya daga adalcinsa ya yi zunubi ya kuma aikata abubuwa masu banƙyamar da mugun mutum ke aikatawa, zai rayu? Babu abubuwan adalcin da ya aikata da za a tuna da su. Saboda rashin amincinsa da kuma saboda zunubai da ya yi, zai mutu.
25 “Duk da haka kun ce, ‘Hanyar Ubangiji ba daidai ba ce.’ Ka ji, ya gidan Isra’ila. Hanyata ba daidai ba ce?
26 In mai adalci ya juye daga adalcinsa ya yi zunubi, zai mutu saboda wannan; saboda zunubin da ya yi, zai mutu.
27 Amma in mugun mutum ya juye daga muguntarsa ya kuma yi abin da yake daidai da kuma gaskiya, zai ceci ransa.
28 Domin ya lura da dukan laifofin da ya yi ya kuma juye daga gare su, tabbatacce zai rayu; ba zai mutu ba.
29 Duk da haka mutanen Isra’ila sun ce, ‘Hanyar Ubangiji ba daidai ba ce.’ Hanyoyina ba daidai ba ne, ya gidan Isra’ila? Ba hanyoyinku ne ba daidai ba?
30 “Saboda haka, ya gidan Isra’ila, zan hukunta ku, kowa bisa ga hanyarsa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Ku tuba! Ku juye daga dukan laifofinku; sa’an nan zunubi ba zai zama sanadin fāɗuwarku ba.
31 Ku raba kanku da dukan laifofin da kuka yi, ku sami sabuwar zuciya da sabon ruhu. Don me za ku mutu, ya gidan Isra’ila?
32 Gama ba na jin daɗin mutuwar wani, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Ku tuba don ku rayu!