6
1 Na ga wani mugun abu a duniya, ya kuma nawaita wa mutane ƙwarai.
2 Allah yakan ba mutum dukiya, da wadata da kuma girma, don kada yă rasa abin da ransa yake so, amma Allah bai ba shi zarafin more su ba, a maimakon haka ma sai baƙo ne yă more su. Wannan ba shi da amfani, mugun abu ne ƙwarai.
3 Mutum zai iya kasance da ’ya’ya ɗari, yă kuma yi shekaru masu yawa; duk da haka kome daɗewarsa, in bai more wadatarsa ba, bai kuma sami kyakkyawar binnewa ba, na ce, gara wanda aka haife shi gawa.
4 Haihuwa ba tă amfane wanda aka haifa gawa ba, gama ya zo daga duhu ya koma duhu inda aka manta da shi.
5 Ko da yake bai ga hasken rana ba, bai kuma san kome ba, duk da haka ya dai huta, fiye da mutumin da bai more wa ransa ba,
6 ko da ya yi shekara dubu biyu amma bai more wadatarsa ba. Ba wuri ɗaya dukansu biyu za su tafi ba?
7 Dukan ƙoƙarin da mutum yake yi, yana yi ne domin bakinsa,
duk da haka bai taɓa gamsar da abin da yake marmari.
8 Da me mai hikima ya fi wawa?
Wace riba ce matalauci yakan samu don yă iya zama da mutane?
9 Gara abin da ido ya gani
da kwaɗayin da bai sami biyan bukata ba.
Wannan ma ba shi da amfani,
naushin iska ne kawai.
10 Duk abin da ya kasance, to, yana da suna,
kuma duk abin da mutum yake, an riga an sani.
Ba mutumin da zai iya ƙarawa
da wanda ya fi shi ƙarfi.
11 Yadda yawan magana take
haka ƙarancin amfaninta,
yaya wannan zai amfane wani?
12 Gama wa ya san abin da ya fi dacewa ga mutum a ’yan kwanakinsa marasa amfani da sukan wuce kamar inuwa? Wa kuma zai iya faɗa masa abin da zai faru a duniya bayan ya rasu?