4
Zalunci, wahalar aiki da rashin abokantaka
1 Na sāke dubawa sai na ga zaluncin da ake yi a duniya.
Na ga hawayen waɗanda ake zalunta
kuma ba su da mai taimako;
masu iko suna goyon bayan masu zalunci,
ga shi ba su da mai taimako.
2 Sai na furta cewa matattu,
waɗanda suka riga suka mutu,
sun fi waɗanda suke a raye farin ciki,
waɗanda har yanzu suke da rai.
3 Amma wanda ya fi su duka
shi ne wanda bai riga ya kasance ba,
wanda bai ga muguntar
da ake yi a duniya ba.
4 Sai na gane cewa, duk wata fama da duk wata nasara sun samo asali daga kishin da mutum yake yi na maƙwabcinsa ne. Wannan ma ba shi da amfani, naushin iska ne kawai.
5 Wawa yakan kame hannuwansa
yă kuma lalatar da kansa.
6 Gara tafin hannu guda cike da kwanciyar rai
da tafin hannu biyu cike da tashin hankali
da harbin iska kawai.
7 Na kuma ga wani abu marar amfani a duniya.
8 Akwai wani mutum shi kaɗai;
bai shi da ɗa ko ɗan’uwa.
Ba shi da hutu daga wahalarsa,
duk da haka bai ƙoshi da dukiyarsa ba.
Ya tambayi kansa, “Ma wane ne nake wannan wahala,
kuma me ya sa nake hana kaina jin daɗi?”
Wannan ma ba shi da amfani,
harkar baƙin cikin ne kawai!
9 Biyu sun fi ɗaya,
gama suna samun riba mai kyau na aikinsu.
10 In ɗaya ya fāɗi,
abokinsa zai taimake shi yă tashi.
Amma abin tausayi ne ga mutumin da ya fāɗi
ba shi kuma da wanda zai taimake shi yă tashi!
11 In mutum biyu sun kwanta tare, za su ji ɗumin juna.
Amma yaya mutum ɗaya zai ji ɗumi yana shi kaɗai?
12 Ana iya shan ƙarfin mutum ɗaya,
mutum biyu za su iya kāre kansu.
Igiya riɓi uku tana da wuya tsinkawa.
Cin gaba ba shi da amfani
13 Gara saurayi wanda yake matalauci amma yake da hikima da sarkin da ya tsufa mai wauta, wanda ba ya karɓar shawara.
14 Yana yiwuwa saurayin yă fito daga kurkuku yă hau gadon sarauta, ko kuma dai an haife shi cikin talauci a ƙasarsa.
15 Na ga cewa dukan waɗanda suka rayu suka kuma yi tafiya a duniya sun bi saurayin, magājin sarkin.
16 Babu ƙarshe ga dukan mutanen da suka riga su. Amma waɗanda suka zo daga baya, ba su gamsu da magājin ba. Wannan ma ba shi da amfani, naushin iska ne kawai.