32
Ku saurara, ya ku sammai, zan yi magana;
bari duniya ta ji maganar bakina.
Bari koyarwata tă zubo kamar ruwan sama
kalmomina kuma su sauko kamar raɓa,
kamar yayyafi a kan sabuwar ciyawa,
kamar ruwan sama mai yawa a kan tsirai marasa ƙarfi.
 
Zan yi shelar sunan Ubangiji.
Ku yabi girman Allahnmu!
Shi Dutse ne, ayyukansa cikakku ne,
dukan hanyoyinsa kuwa masu adalci ne.
Allah mai aminci, wanda ba ya yin rashi gaskiya,
shi mai adalci ne, nagari ne kuma.
 
Sun aikata mugunta a gabansa;
saboda abin kunyarsu, su ba ’ya’yansa ba ne,
amma wata muguwar tsara ce, karkatacciya.
Haka za ku biya Ubangiji,
Ya ku wawaye da kuma mutane marasa hikima?
Shi ba Ubanku ba ne, Mahaliccinku,
wanda ya yi ku, ya kuma siffanta ku?
 
Ku tuna da kwanakin dā,
ku tuna da tsararrakin da suka wuce tun tuni,
Ku tambayi iyayenku, za su faɗa muku,
dattawanku, za su kuma bayyana muku.
Sa’ad da Mafi Ɗaukaka ya ba da al’ummai gādonsu,
sa’ad da ya raba dukan ’yan adam,
ya kafa iyakoki wa mutane
bisa ga yawan ’ya’yan Isra’ila maza.
Gama rabon Ubangiji shi ne mutanensa,
Yaƙub shi ne rabon gādonsa.
 
10 A cikin hamada ya same shi,
a jeji marar amfani, inda namomi suke kuka.
Ya tsare shi, ya kuma lura da shi;
ya bi da shi kamar ƙwayar idonsa,
11 kamar gaggafar da take yawo a kan sheƙarta
tana rufe ’ya’yanta,
ta buɗe fikafikanta don tă kwashe su
tă ɗauke su a kafaɗunta.
12 Ubangiji kaɗai ya jagorance shi;
babu wani baƙon gunkin da yake tare da shi.
 
13 Ya sa shi ya hau ƙwanƙolin dutse
ya ciyar da shi da amfanin gona.
Ya shayar da shi da zuma daga dutse,
da kuma mai daga dutsen ƙanƙara,
14 da kindirmo da madara daga shanu da tumaki
da ƙibabbun tumaki da awaki,
da zaɓaɓɓun ragunan Bashan
da kuma ƙwayoyin alkama mafi kyau.
Ka sha ruwan inabi ja wur mai kumfa.
 
15 Yeshurun* ya yi ƙiba, ya yi kauri;
cike da abinci, ya zama da nauyi, ya kuma zama sumul.
Ya yashe Allahn da ya yi shi,
ya ƙi Dutse Cetonsa.
16 Suka sa shi kishi saboda baƙin allolinsu,
suka husata shi da gumakan banƙyamarsu.
17 Suka yi hadaya ga aljanu, waɗanda ba Allah ba,
ga allolin da ba su sani ba,
ga allolin da aka shigo da su daga baya,
allolin da kakanninku ba su ji tsoronsu ba.
18 Kuka rabu da Dutsen da ya zama mahaifi gare ku;
kuka manta da Allahn da ya haife ku.
 
19 Ubangiji ya ga wannan ya kuma ƙi su,
domin ’ya’yansa maza da mata sun husata shi.
20 Ya ce, “Zan ɓoye fuskata daga gare su,
in ga ƙarshensu;
gama su muguwar tsara ce,
’ya’ya ne marasa aminci.
21 Sun sa ni kishi ta wurin abin da ba allah ba,
suka kuma husata ni da gumakansu na wofi.
Zan sa su yi kishi ta wurin waɗanda ba mutane ba;
zan sa su yi fushi ta wurin al’ummar da ba ta da sani.
22 Gama fushina ya kama wuta,
tana ci har ƙurewar zurfin lahira.
Za tă cinye duniya da girbinta,
tă kuma sa wuta a tussan duwatsu.
 
23 “Zan tula masifu a kansu
in kuma gama kibiyoyina a kansu.
24 Zan aika da yunwa mai tsanani a kansu,
zazzaɓi mai zafi da muguwar annoba;
zan aika da haƙoran namun jeji a kansu,
da dafin mesa masu ja da ciki.
25 Waɗanda suke a waje, takobi zai kashe su,
a cikin gidajensu kuma tsoro zai mamaye su.
’Yan maza da ’yan mata za su hallaka,
haka ma jarirai da maza masu furfura.
26 Na ce zan watsar da su
in sa a manta da su a tunanin ’yan adam.
27 Amma ina tsoron tsokanar abokin gāba,
don kada abokan gāba su kāsa ganewa
har su ce, ‘Hannunmu ne ya yi nasara;
ba Ubangiji ne ya aikata dukan wannan ba.’ ”
 
28 Al’ummai ne marasa azanci,
babu ganewa a cikinsu.
29 A ce su masu hikima ne har su gane wannan
su gane abin da ƙarshensu zai zama!
30 Yaya mutum guda zai kore dubu,
mutum biyu su sa dubu goma su gudu,
sai ko Dutsensu ya sayar da su,
sai ko Ubangiji ya bashe su.
31 Gama dutsensu ba kamar Dutsenmu ba ne,
abokan gābanmu sun san da haka.
32 Kuringarsu ta fito daga kuringar Sodom ne,
daga gonakin Gomorra kuma.
’Ya’yan inabinsu dafi ne,
nonnansu masu ɗaci ne.
33 Ruwan inabinsu dafin macizai ne,
mugun dafin gamshaƙa ne.
 
34 “Ban jibge wannan a ma’ajiya
na kuma yimƙe shi a taskokina ba?
35 Sakayya nawa ne, zan kuwa ɗau fansa.
A cikin lokaci, ƙafarsu za tă yi santsi;
ranar masifarsu ta yi kusa
hallakarsu kuma tana gaggautawa a kansu.”
 
36 Ubangiji zai shari’anta mutanensa
yă kuma ji tausayin bayinsa
sa’ad da ya ga ƙarfinsu ya ƙare
babu kowa kuma da ya rage, bawa ko ’yantacce.
37 Zai ce, “To, ina allolinsu,
dutsen da suka yi mafaka a ciki,
38 allolin da suka ci kitsen hadayunsu
suka kuma sha ruwan inabin hadayunsu?
Ku sa su tashi su taimake ku mana!
Bari su ba ku mafaka!
 
39 “Ku duba yanzu cewa ni ne Shi!
Ba wani allah in ban da ni.
Nakan kashe in kuma rayar,
nakan sa rauni in kuma warkar,
ba wanda yake da iko yă cece wani daga hannuna.
40 Na ɗaga hannu sama na kuma furta.
Muddin ina raye har abada,
41 sa’ad da na wasa takobi mai walƙiya
hannuna kuwa ya cafke shi don yin hukunci,
zan ɗau fansa a kan abokan gābana
in sāka wa waɗanda suke ƙina.
42 Zan sa kibiyoyina su bugu da jini,
yayinda takobina yana cin nama,
jinin kisassu da na kamammu,
kawunan shugabannin abokan gāba.”
 
43 Ku yi farin ciki, ya ku al’ummai, tare da mutanensa,
gama zai rama ɗau fansar jinin bayinsa;
zai ɗau fansa a kan abokan gābansa
yă kuma yi kafara domin ƙasarsa da mutanensa.
44 Sai Musa ya zo da Yoshuwa ɗan Nun suka faɗa dukan waɗannan kalmomi wannan waƙa a kunnen mutane. 45 Sa’ad da Musa ya gama karanta waɗannan kalmomi ga dukan Isra’ila, 46 ya ce musu, “Ku riƙe dukan kalmomin da na furta muku a yau, don ku umarce ’ya’yanku su lura, su yi biyayya da dukan kalmomin wannan doka. 47 Ba kalmomi kurum ba ne dominku, amma har ranku ma. Ta wurinsu za ku yi tsawon rai a ƙasar da kuke haye Urdun ku ci gādonta.”
Musa ya mutu a kan Dutsen Nebo
48 A wannan rana Ubangiji ya ce wa Musa, 49 “Ka hau Duwatsun Abarim zuwa Dutsen Nebo a Mowab, tsallake daga Yeriko, ka hangi Kan’ana, ƙasar da nake ba wa Isra’ilawa gādo. 50 A can kan dutsen da ka hau za ka mutu a kuma tara ka ga mutanenka, kamar yadda ɗan’uwanka Haruna ya mutu a Dutsen Hor aka kuma tara shi ga mutanensa. 51 Wannan kuwa domin ku biyu kun fid da aminci gare ni a gaban Isra’ilawa a ruwan Meriba ta Kadesh, a Hamadar Zin kuma saboda ba ku riƙe tsarkina a cikin Isra’ilawa ba. 52 Saboda haka, za ka ga ƙasar daga nesa kawai; ba za ka shiga ƙasar da nake ba wa mutanen Isra’ila ba.”
* 32:15 Yeshurun yana nufin mai adalci, wato, Isra’ila. 32:43 Ko kuwa Ku sa mutanensa su yi farin ciki, ya al’ummai 32:44 Da Ibraniyanci Hosheya, wani sunan Yoshuwa.