5
Rubutu a kan bango
Sarki Belshazar ya yi babban biki domin dubban hakimansa ya kuma sha ruwan inabi tare da su. Yayinda Belshazar yake shan ruwan inabi, sai ya umarta a kawo zinariya da azurfan da Nebukadnezzar mahaifinsa* ya kwaso daga haikali a Urushalima, saboda sarki da hakimansa, da matansa da ƙwarƙwaransa su sha da su. Sai suka kawo kayan zinariyan nan da aka kwaso daga haikalin Allah a Urushalima, sarki kuwa da hakimansa, da matansa, da ƙwarƙwaransa suka yi ta sha da su. Yayinda suke shan ruwan inabin, sai suka yabi allolin zinariya da azurfa, da na tagulla, da na ƙarfe, da na itace da kuma na dutse.
Nan da nan sai ga yatsotsin hannun mutum sun bayyana, suna yin rubutu a kan shafen bangon, kusa da wurin da ake ajiye fitilar fadar sarki. Sarki kuwa yana ganin hannun yayinda yake rubutu. Sai fuskarsa ta ruɗe, ya kuma ji tsoro ƙwarai har gwiwoyinsa suka yi ta bugun juna, ƙafafunsa kuma suka rasa ƙarfi.
Sai sarki ya kira masu dabo, masanan taurari da masu duba, a kawo su, ya kuma ce wa masu hikima na Babilon, “Duk wanda ya karanta wannan rubutu ya kuma faɗa mini abin da yake nufi, za a sa masa rigar shunayya, a kuma sa masa sarƙar zinariya a wuyansa, zai zama na uku a cikin masu mulkin ƙasar.”
Sa’an nan sai dukan masu hikima suka zo ciki, amma ba su iya karanta rubutun ba ko su faɗa wa sarki abin da yake nufi. Saboda haka Sarki Belshazar ya firgita ƙwarai kuma fuskarsa ta ƙara ruɗewa. Hakimansa kuma suka rikice.
10 Sai sarauniya, da jin muryoyi na sarki da na hakimansa, ta shiga babban ɗakin liyafar. Ta ce, “Ya sarki, ranka yă daɗe! Kada ka firgita! Kada fuskarka ta ruɗe! 11 Akwai wani mutum a masarautarka wanda yake da ruhun alloli masu tsarki a cikinsa. A zamanin mahaifinka an gane cewa yana da basira da hazaka da hikima kamar na alloli. Sarki Nebukadnezzar mahaifinka, mahaifinka sarki, na ce, ya naɗa shugaban masu dabo, da masu sihiri, masanan taurari da kuma masu duba. 12 Wannan mutum Daniyel, wanda sarki ya kira Belteshazar, an gane yana da ruhu nagari, da ilimi, da ganewa don yin fassarar mafarkai, da bayyana ma’anar kacici-kacici, da warware al’amura masu wuya. Ka kira Daniyel shi kuwa zai faɗa maka abin da rubutun nan yake nufi.”
13 Saboda haka aka kawo Daniyel a gaban sarki, sai sarki ya ce masa, “Kai ne Daniyel ɗin nan, ɗaya daga cikin kamammu waɗanda mahaifina sarki ya kawo daga Yahuda? 14 Na sami labari cewa kana da ruhun alloli a cikinka da kuma basira, da hazaka da kuma fitacciyar hikima. 15 An kawo masu hikima da masu dabo a gabana domin su karanta wannan rubutu su kuma faɗa mini abin da yake nufi, amma ba su iya ba. 16 Na sami labari cewa kana iya ba da fassara da kuma warware matsaloli masu wuya. In har ka iya karanta wannan rubutun ka kuma faɗa mini abin da yake nufi, za a sa maka riga shunayya, a kuma sa sarƙar zinariya a wuyanka. Za ka zama na uku a cikin masu mulkin ƙasar.”
17 Sai Daniyel ya amsa wa sarki ya ce, “Za ka iya ajiye kyautar wa kanka ko kuma ka ba wa wani. Duk da haka, zan karanta wa sarki rubutun, in kuma faɗa abin da yake nufi.
18 “Ya sarki, Allah Mafi Ɗaukaka ya ba mahaifinka Nebukadnezzar sarauta, da girma, da ɗaukaka, da martaba. 19 Saboda irin matsayin da ya ba shi, dukan mutane da al’ummai da kuma dukan harsuna suka ji tsoronsa suka yi rawar jiki a gabansa. Bisa ga ganin damarsa yakan kashe wani, ya bar wani da rai, haka kuma yakan ɗaukaka wani, ya ƙasƙantar da wani. 20 Amma da lokacin da zuciyarsa ta cika da girman kai ta kuma taurare, sai aka kore shi daga gadon sarautarsa, aka raba shi kuma da darajarsa. 21 Aka kore shi daga cikin mutane aka kuma ba shi tunani irin na dabba; ya yi zama tare da jakunan jeji, ya kuma ci ciyawa kamar shanu; jikinsa kuma ya jiƙe da raɓa, har zuwa lokacin da ya gane, ashe, Allah Maɗaukaki ne mai iko duka a kan dukan mulkoki a duniya, yake kuma ba da mulki ga duk wanda ya ga dama.
22 “Amma kai ɗansa,§ Ya Belshazar, ba ka ƙasƙantar da kanka ba, ko da yake ka san wannan duka. 23 A maimakon, sai ka nuna wa Ubangiji na sama girman kai. Ka sa aka kawo maka su kwaf na zinariya daga haikalinsa, da kai da hakimanka, da matanka da ƙwarƙwaranka kuka sha ruwan inabi da su. Kuka yabi allolin zinariya da na azurfa, da na tagulla, da na baƙin ƙarfe, da na itace, da na dutse waɗanda ba sa ji, ba sa gani, ba sa da gane kome. Amma ba ka girmama Allah ba, wanda ranka da dukan harkokinka suna a hannunsa. 24 Saboda haka ya aiko da hannun da ya yi rubutun nan.
25 “Wannan shi ne rubutun da aka yi,
Mene, mene, tekel, farsin
26 “Abin da kalmomin nan suke nufi shi ne,
“Mene*, Allah ya ƙayyade yawan kwanakin mulkinka ya kuma kawo su ga ƙarshe.
27  “Tekel, An kuma auna ka a ma’auni aka tarar ka kāsa.
28  “Feres, An raba mulkinka aka ba wa Medes da Farisa.”
29 Sai Belshazar ya umarta, aka sa wa Daniyel riga mai shunayya, aka sa sarƙar zinariya a wuyansa, aka kuma yi shela, cewa yanzu shi ne na uku a cikin masu mulkin ƙasar.
30 A wannan dare aka kashe Belshazar, sarkin Babiloniyawa,§ 31 Dariyus mutumin Medes kuwa ya karɓi mulkin, yana da shekara sittin da biyu.
* 5:2 Ko kakansa; ko wanda ya gāji sarauta daga gare shi; haka kuma a ayoyi 11, 13, da 18 5:7 Ko kuwa Kaldiyawa, haka ma a aya 11 5:10 Ko kuwa mahaifiyar sarauniya § 5:22 Ko zuriya; ko magāji * 5:26 Mene yana iya nufin ƙididdigewa Ko kuwa mina (ko kashi na kuɗi). 5:27 Tekel yana iya nufin awo Ko kuwa shekel. 5:28 Feres (jumli ne na Farsin) yana iya nufin an raba Ko kuwa Farisa Ko kuwa rabin mina Ko kuwa rabin shekel. § 5:30 Ko kuwa Kaldiyawa