6
Kaito ga zaman sakewa
Taku ta ƙare, ku da kuke zaman sakewa a Sihiyona,
da ku waɗanda kuke ji zama a Dutsen Samariya lafiya ne,
ku manyan mutanen ƙasar da take sananniya,
waɗanda mutanen Isra’ila suke zuwa!
Ku je Kalne ku dube ta;
ku wuce daga can zuwa Hamat-rabba,
sa’an nan ku gangara zuwa Gat a Filistiya.
Sun fi masarautunku biyu ne?
Ƙasarsu ta fi taku girma?
Kuna ƙoƙari ku kauce wa wannan muguwar rana
kuna kuma jawo mulkin tashin hankali kusa.
Kuna kwanciya a kan gadajen da aka yi musu shimfiɗar hauren giwa
kuna mimmiƙe a kan kujerunku.
Kuna cin naman ƙibabbun raguna
da na ƙosassun ’yan maruƙa.
Kuna kaɗa molayenku yadda Dawuda ya yi
kuna ƙirƙiro waƙoƙi a kan kayan kaɗe-kaɗe.
Da manyan kwanoni kuke shan ruwan inabi
kuna kuma shafa mai mafi kyau,
amma ba kwa baƙin ciki game da kangon da Yusuf ya zama.
Saboda haka za ku zama na farkon da za su tafi zaman bauta;
bukukkuwanku da shagulgulanku za su ƙare.
Ubangiji yana ƙyamar girmankan Isra’ila
Ubangiji Mai Iko Duka da kansa ya rantse, Ubangiji Allah Maɗaukaki ya furta,
“Ina ƙyamar girman kan Yaƙub,
ba na kuma son kagarunsa;
zan ba da birnin
da duk abin da yake cikinta.”
Ko da mutum goma ne suka ragu a gida guda, su ma za su mutu. 10 In kuma wani dangi ya shiga don yă fitar da gawawwakin yă ƙone ya kuwa tambayi wani wanda yake ɓoye a can, yana cewa, “Akwai wani tare da kai?” Ya kuwa ce, “Babu,” sai yă ce, “Kul! Kada mu ambaci sunan Ubangiji.”
11 Gama Ubangiji ya ba da umarni,
zai kuma ragargaza babban gidan nan kucu-kucu
ƙaramin gidan kuwa zai yi rugu-rugu da shi.
 
12 Dawakai sukan yi gudu a kan duwatsu?
Wani yana iya yin noma a teku da shanun noma?
Amma ga shi kun mai da gaskiya ta zama dafi
amfanin adalci kuma ya zama ɗaci,
13 ku da kuke murna saboda an ci Lo Debar* da yaƙi
kuka kuma ce, “Ba da ƙarfinmu ne muka ƙwace Karnayim ba?”
 
14 Gama Ubangiji Allah Maɗaukaki ya ce,
“Zan sa wata ƙasa ta tayar muku, ya ku gidan Isra’ila,
wadda za tă matsa muku tun
daga Lebo Hamat zuwa kwarin Araba.”
* 6:13 Lo Debar yana nufin wofi. 6:13 Karnayim yana nufin ƙahoni; ƙaho a nan yana a matsayin ƙarfi. 6:14 Ko kuwa daga mashigi zuwa