28
Tsibirin Malta
Bayan da muka kai bakin tekun lafiya, sai muka tarar cewa sunan tsibirin Malta ne. Mutanen tsibirin kuwa suka nuna mana babban alheri. Suka hura wuta suka marabce mu duka saboda ana ruwan sama da kuma sanyi. Bulus ya tattara tarin itace, yayinda kuma yake sa itacen a wuta, sai maciji ya ɓullo saboda zafi, ya dāfe a hannunsa. Da mutanen tsibirin suka ga macijin yana lilo a hannunsa, sai suka ce wa juna “Lalle, wannan mutum mai kisankai ne; gama ko da yake ya tsira daga teku, Adalci bai bar shi ya rayu ba.” Amma Bulus ya karkaɗe macijin a cikin wuta, bai kuwa ji wani ciwo ba. Mutanen kuma suka yi zato zai kumbura ko kuma nan da nan zai fāɗi matacce, amma da aka daɗe ba su ga wani abu ya faru da shi ba, sai suka sāke ra’ayi suka ce shi wani allah ne.
Akwai wani filin nan kusa wanda yake na Fubiliyus, babban shugaban tsibirin. Shi ne ya karɓe mu a gidansa da alheri ya kuma ciyar da mu har kwana uku. Mahaifinsa kuwa yana kwanciya a gado yana fama da zazzaɓi da atuni. Bulus ya shiga ciki don yă gan shi, bayan ya yi masa addu’a, sai ya ɗibiya masa hannuwa ya warkar da shi. Sa’ad da wannan ya faru, sauran marasa lafiya a tsibirin suka zo aka kuma warkar da su. 10 Suka girmama mu ta kowane hali da muka shirya za mu tashi, sai suka ba mu abubuwan da muke bukata.
Isowa a Roma
11 Bayan wata uku sai muka tashi a wani jirgin ruwan da ya ci damina a tsibirin. Jirgin ruwa kuwa na Alekzandariya ne yana da siffar tagwayen allolin Kasto da Follus. 12 Muka isa Sirakus a can muka yi kwana uku. 13 Daga can muka tashi muka isa Regiyum. Kashegari iskar kudu ta taso, kashegari kuma muka kai Futeyoli. 14 A can muka tarar da waɗansu ’yan’uwa waɗanda suka gayyaci mu mu yi mako ɗaya da su. Da haka dai muka kai Roma. 15 ’Yan’uwan da suke can sun sami labari cewa muna zuwa, sai suka tashi tun daga Kasuwar Affiyus da Masauƙi Uku don su tarye mu. Da ganin mutanen nan sai Bulus ya gode wa Allah ya kuma sami ƙarfafawa. 16 Da muka isa Roma, sai aka yarda wa Bulus yă zauna shi kaɗai, tare da sojan da zai yi gadinsa.
Bulus ya yi wa’azi a Roma a tsare
17 Bayan kwana uku sai ya kira taron shugabannin Yahudawa. Da suka taru, Bulus ya ce musu, “’Yan’uwana, ko da yake ban yi wa mutanenmu wani laifi ba ko kuma wani abu game da al’adun kakanninmu, aka kama ni a Urushalima aka kuma ba da ni ga Romawa. 18 Suka tuhume ni suka kuma so su sake ni, domin ba a same ni da wani laifin da ya cancanci kisa ba. 19 Amma da Yahudawa suka ƙi, sai ya zama mini dole in ɗaukaka ƙara zuwa gaban Kaisar ba don ina da wani zargin da zan kawo game da mutanena ba. 20 Saboda wannan ne na nemi in gan ku in kuma yi magana da ku. Saboda begen Isra’ila ne, nake a daure da wannan sarƙa.”
21 Suka amsa cewa, “Ba mu sami wani wasiƙa daga Yahudiya game da kai ba, kuma ba kowa daga cikin ’yan’uwan da suka zo daga can ya kawo wani labari ko ya faɗi wani mummuna abu game da kai. 22 Amma muna so mu ji ra’ayinka, gama mun san cewa mutane ko’ina suna muguwar magana a kan wannan ɗarikar.”
23 Suka shirya su sadu da Bulus wata rana, suka ma zo da yawa fiye da dā a wurin da Bulus yake zama. Daga safe har zuwa yamma ya yi ta yin musu bayani, ya kuma shaida musu mulkin Allah yana ƙoƙarin rinjayarsu game da Yesu daga Dokar Musa da kuma daga Annabawa. 24 Waɗansu suka rinjayu da abin da ya faɗa, amma waɗansu suka ba su gaskata ba. 25 Suka kāsa yarda da juna suka fara watsewa bayan Bulus ya yi wannan magana guda cewa, “Ruhu Mai Tsarki ya faɗa wa kakannin-kakanninku gaskiya sa’ad da ya ce ta bakin annabi Ishaya cewa,
26 “ ‘Je ka wurin mutanen nan ka ce,
“Za ku yi ta ji amma ba za ku fahimta ba;
za ku yi ta dubawa, amma ba za ku gani ba.”
27 Gama zuciyar mutanen nan ta yi tauri;
da ƙyar suke ji da kunnuwansu,
sun kuma rufe idanunsu.
In ba haka ba za su iya gani da idanunsu,
su ji da kunnuwansu,
su fahimta a zukatansu,
su kuma juyo, in kuwa warkar da su.’*
28 “Saboda haka na so ku san cewa an aika da ceton Allah ga Al’ummai, za su kuwa saurara!”
30 Shekaru biyu cif Bulus ya zauna a can a gidansa na haya yana marabtar duk wanda ya je wurinsa. 31 Ya yi wa’azin mulkin Allah yana kuma koyarwa game da Ubangiji Yesu Kiristi, gabagadi ba tare da wani abu ya hana shi ba.
* 28:27 Ish 6.9,10 28:28 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā suna da saurara! 29 Bayan ya faɗi haka, sai Yahudawa suka watse, suna gardama mai zafi a tsakaninsu