19
Bulus a Afisa
1 Lokacin da Afollos yake a Korint, Bulus ya bi hanyar da ta ratsa ta Asiya ya zo Afisa. A can ya sadu da waɗansu almajirai,
2 sai ya tambaye, su ya ce, “Kun karɓi Ruhu Mai Tsarki sa’ad da kuka gaskata?”
Suka amsa suka ce, “A’a, ba mu ma san akwai Ruhu Mai Tsarki ba.”
3 Saboda haka Bulus ya yi tambaya ya ce, “To, wace baftisma aka yi muku?”
Suka ce, “Baftismar Yohanna.”
4 Bulus ya ce, “Ai, baftismar Yohanna, baftisma ce ta tuba. Ya ce wa mutane su gaskata a wani wanda yake zuwa bayansa, wato, Yesu.”
5 Da ji wannan, sai aka yi musu baftisma a cikin sunan Ubangiji Yesu.
6 Da Bulus ya ɗibiya musu hannuwansa, sai Ruhu Mai Tsarki ya sauka musu, suka kuwa yi magana da harsuna, suka kuma yi annabci.
7 Mutane kuwa su wajen mutum goma sha biyu ne.
8 Bulus ya shiga majami’a ya yi magana gabagadi a can na watanni uku, yana muhawwara yana kuma rinjayarsu game da mulkin Allah.
9 Amma waɗansunsu suka taurara; suka ƙi su gaskata kuma a gaban jama’a suka yi baƙar magana game da Hanyar. Bulus kuwa ya bar su. Ya tafi tare da almajirai ya dinga tattaunawa da su kullum a babban ɗakin jawabi na Tirannus.
10 Wannan ya ci gaba har shekara biyu, sai da ya sa dukan Yahudawa da Hellenawa da suke zaune a lardin Asiya suka ji maganar Ubangiji.
11 Allah ya yi ayyukan banmamakin da suka wuce misali ta hannu Bulus,
12 har ma ana kai hankicif da adikan da suka taɓa jikinsa wa marasa lafiya, suka kuwa warke daga cututtukansu mugayen ruhohi kuma suka rabu da su.
13 Waɗansu Yahudawa masu yawo gari-gari suna fitar da mugayen ruhohi suka yi ƙoƙari su yi amfani da sunan Ubangiji Yesu a kan waɗanda suke da aljanu. Suna cewa, “A cikin sunan Yesu wanda Bulus yake wa’azi, na umarce ku, ku fito.”
14 ’Ya’ya bakwai maza na Sikeba, wani babban firist na Yahudawa, suna yin haka.
15 Wata rana mugun ruhu ya amsa musu ya ce, “Yesu kam na sani, Bulus kuma na sani, amma ku kuma su wane ne?”
16 Sai mutumin da yake da mugun ruhun ya fāɗa musu ya sha ƙarfinsu duka. Ya yi musu dūkan tsiya har suka fita a guje daga gidan tsirara jini yana zuba.
17 Da Yahudawa da Hellenawan da suke zama a Afisa suka ji wannan labari sai duk tsoro ya kama su, aka kuwa darjanta sunan Ubangiji Yesu ƙwarai.
18 Da yawa cikin waɗanda suka gaskata yanzu suka zo a fili suka furta mugayen ayyukansu.
19 Waɗansu masu yin sihiri suka kawo naɗaɗɗun littattafansu wuri ɗaya suka kuwa ƙone su a gaban jama’a. Sa’ad da aka lissafta yawan kuɗin naɗaɗɗun littattafan nan, sai jimillar ta kai darik dubu hamsin.
20 Ta haka maganar Ubangiji ta bazu ko’ina ta kuma yi ƙarfi.
21 Bayan dukan wannan ya faru, sai Bulus ya yanke shawara ya ratsa Makidoniya da Akayya in za shi Urushalima. Ya kuma ce, “Bayan na tafi can, dole in ziyarci Roma ita ma.”
22 Sai ya aiki biyu daga cikin masu taimakonsa, Timoti da Erastus, zuwa Makidoniya, yayinda shi kuwa ya ɗan dakata a lardin Asiya.
Hargitsi a Afisa
23 Kusan wannan lokaci sai aka yi wani babban hargitsi game da wannan Hanyar.
24 Wani maƙerin azurfa, mai suna Demetiriyus wanda yake ƙera siffar ɗakunan tsafin Artemis da azurfa, ba ƙaramin ciniki yake kawo wa mutane masu sana’an nan ba.
25 Sai ya tara su wuri ɗaya, tare da masu irin wannan sana’ar ya ce, “Ku jama’a, kun san muna samun kuɗin shiga sosai daga wannan sana’a.
26 Kuma kuna ji kuna gani yadda Bulus ɗin nan ya shawo kan mutane da yawa ya kuma sa suka bauɗe a nan a Afisa da dukan lardin Asiya. Yana cewa alloli da mutum ya ƙera ba alloli ba ne ko kaɗan.
27 Akwai hatsari, ba kawai cewa sana’armu za tă rasa sunanta mai daraja ba, amma za a yi banza da ɗakin tsafin Artemis alliyarmu mai girma, alliyar kanta wadda ake bauta a ko’ina a yankin Asiya da kuma duniya, za a raba ta da darajarta.”
28 Da suka ji haka, sai suka yi fushi ƙwarai suka fara ihu suna cewa, “Girma ta tabbata ga Artemis ta Afisawa!”
29 Jim kaɗan sai hayaniya ta tashi a dukan birnin. Sai mutane suka cafke Gayus da Aristarkus, abokan tafiyar Bulus daga Makidoniya, suka ruga da zuwa fili da nufi ɗaya.
30 Bulus ya so ya bayyana a gaban taron, amma almajirai ba su bar shi ba.
31 Har waɗansu shugabannin lardin ma, abokan Bulus, suka aika masa suna roƙonsa kada yă kuskura ya shiga filin nan.
32 Taron kuwa ya ruɗe. Waɗansu suna ihu suna ce abu kaza, waɗansu kuma wani abu dabam. Yawancin mutane kuma ba su ma san abin da ya sa suke a wurin ba.
33 Yahudawa suka tura Alekzanda gaba, sai waɗansu a taron suka riƙa yin masa ihu. Sai ya ɗaga hannu don a yi shiru don yă kāre kansa a gaban mutane.
34 Amma sa’ad da suka gane shi mutumin Yahuda ne, sai duk suka yi ihu gaba ɗaya na kusa sa’a biyu, suna cewa, “Girma ta tabbata ga Artemis ta Afisawa!”
35 Sai magatakardar birnin ya sa taron su yi shiru, sa’an nan ya ce, “Mutanen Afisa, ashe duk duniya ba tă san cewa birnin Afisa ce mai lura da haikalin Artemis mai girma da kuma siffarta da ya fāɗi daga sama ba?
36 Saboda haka, da yake ba dama a yi mūsun wannan gaskiya, ya kamata ku natsu kada ku yi kome da garaje.
37 Kun kawo mutanen nan a nan, gashi kuwa ba su yi fashin haikali ba, ba su kuwa saɓa wa alliyarmu ba.
38 To, in haka ne, in Demetiriyus da abokan sana’arsa suna da wata magana game da wani ai, kotuna suna nan a buɗe, akwai kuma muƙaddasai. Suna iya kai ƙara.
39 In kuma akwai wani abu har yanzu da kuke so ku kawo, dole a daidaita shi a majalisa.
40 Yadda yake a yanzu, muna a hatsarin amsa zargin ta da hargitsi saboda abin da ya faru yau. Da yake ba za mu iya ba da dalilin da ya sa aka yi wannan hargitsi ba.”
41 Bayan da ya faɗi haka, sai ya sallami taron.